Aƙalla ‘yan ci-rani 19 sun mutu bayan dubban mutane sun yi ƙoƙarin tsallakewa daga Maroko zuwa cikin yankin Sifaniya da ke yankunan arewacin Afirka na Ceuta da Melilla, in ji ‘yansandan Sifaniya da kafafan watsa labaran cikin ƙasar.
Kafafan watsa labaran Sifaniya sun ba da rahoton cewa dubban ‘yan ci-rani sun tsallake cikin Ceuta a cikin ‘yan kwanakinnan, lamarin da ya sa Sifaniya ta tura sojoji domin tallafa wa jami’an tsaron farin kaya da kuma tsaura tsaron bakin iyaka.
Sifaniya ta kuma rufe hanyar kan iyakar Beni Enzar zuwa Maroko a Melilla ranar Alhamis bayan ɗaruruwan ‘yan ci-rani suka yi ƙoƙarin shiga yankin ta kan ƙasa da kuma ta ruwa. Shugaban Melilla Juan Jose Imbroda ya ce hukumomi sun shawo kan yawancin matsalolin tare da haɗin kan dakarun tsaron Maroko.
Daga farko dai ranar Jumma’a, hukumomin Maroko sun hana dubban mutane kaiwa kan iyakar, inda suka dakatar da da yawa kusa da birnin arewaci na Fnideq da kuma janye su ta ababen hawa daga yankin.
Tsallakewa na mutane da yawa na zuwa ne kwanaki bayan Sifaniya da Maroko sun cim ma matsaya ta ƙarfafa haɗin-kai da kuma gaggauta komawar ‘yan ci-rani da ke shiga Ceuta ba bisa ƙa’ida ba.
Maroko ba ta yi tsokaci ba tukunna game da rahotannin mace-macen ko kuma yarjejeniyar komawar. ‘Yan ci-rani da yawa daga Maroko da sauran ƙasashen Afirka sun yi ƙoƙarin tsallakewa mai cike da hatsari zuwa Turai don neman ingantattun damarmaki na arziki.















