| Hausa
DUNIYA
4 minti karatu
Iran na shirin kai harin bam mai ɗauke sinadarai masu guba kan babban birnin Amurka - Rahoto
Wasu sabbin bayanan sirrin Amurka sun nuna cewa Iran na nazarin matakan da za ta iya ɗauka, maimakon shirin kai hari nan-take kan Washington DC, duk da cewa an daƙile shirye-shiryen kai hari kan wasu muhimman wurare da aka gano.
Iran na shirin kai harin bam mai ɗauke sinadarai masu guba kan babban birnin Amurka - Rahoto
Fadar White House na Amurka da ke Washington / Reuters (Wire)

Hukumomin leƙen asirin Amurka sun gano wasu shirye-shirye da ake zargin Iran na yi, na kai hare-hare kan manyan jami'an gwamnatin Shugaban Amurka, Donald Trump a Washington, DC, ta hanyar amfani da bam mai ɗauke da sinadarai masu guba.

Kafar watsa labarai CNN ce ta ruwaito wannan bayani bisa bayanan jami'an Amurka bakwai da ke da masaniya kan lamarin.

Rahotannin sun janyo ƙarin fargabar tsaro da kuma shirin tunkarar duk wani hari da ka iya faruwa a cikin gwamnatin Amurka, duk da cewa jami'ai na da saɓanin ra'ayi kan ko Iran na da ƙarfin aiwatar da irin wannan hari ko kuma tana niyyar yin hakan.

A cewar CNN, majiyoyin da suka san bayanan sirrin sun bayyana ayyukan Iran a matsayin ƙoƙarin tsara hanyoyin da za ta iya kai hari, ba wai tana shirin kai hari nan-take ba ne.

Ko da yake, wasu majiyoyi biyu sun ce shirye-shiryen sun bayyana takamaiman wurare da kuma mutanen da za a kai wa hari a babban birnin Amurka.

Masu AlakaTRT Afrika - Jiragen dakon mai uku sun taka nakiyoyin da aka dasa a Mashigar Ruwan Hormuz

Kakakin Fadar White House, Lauren Bis, ta ce gwamnatin Amurka na sa ido kan duk wata barazana da ka iya tasowa, amma ta jaddada cewa babu wata barazana ta gaggawa da aka tabbatar ƙasar na fuskanta a halin yanzu.

"Muna sa ido kan duk wata barazana da za ta iya tasowa, amma a halin yanzu babu wata sahihiyar barazana da ƙasar ke fuskanta," in ji Bis.

Rahotanni sun ce bayanan sirrin sun sanya jami'an Amurka gudanar da tarurruka da dama a makon da ya gabata domin tattauna yiwuwar matakan mayar da martani da kuma hanyoyin daƙile hare-haren.

Wata majiya da ke da masaniya kan bayanan sirrin ta bayyana shirye-shiryen tunkarar yiwuwar harin a matsayin wasu matakai na taka-tsantsan, yayin da wata majiyar ta ce jami'ai na ci gaba da muhawara kan ko Iran na da mutanen da za su iya aiwatar da irin wannan hari.

Batun tsaron ya kuma shafi matakan kariya ga manyan jami'an gwamnatin Amurka.

A cewar CNN, an mayar da sakataren baitulmalin Amurka, Scott Bessent, zuwa gidan sojoji a makon da ya gabata sakamakon barazanar tsaro da ake alakantawa da Iran.

Ofishin jakadancin Iran a Majalisar Ɗinkin Duniya da ke New York ya yi watsi da zargin cewa Tehran na shirin amfani da makamai masu guba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, ofishin ya ce, ‘‘ daukar matakin amfani da makamai masu guba a kowane yanayi a matsayin abin da bai dace ba, tare da yin watsi da zarge-zargen da ya bayyana a matsayin ƙarya da ƙirƙira.’’

Sa ido kan barazanar

Jami'an Amurka biyu sun shaida wa CNN cewa hukumomin leƙen asirin ƙasar na sa ido kan duk wani shiri da ke nuna Iran na iya daukar matakin amfani da makamai masu guba kan sojojin Amurka da ke sansanonin soji a Gabas ta Tsakiya.

Wannan damuwa ta haifar da wani shirin ko-ta-kwana na daban domin tabbatar da cewa jami’an diflomasiyya da na eƙen asirin Amurka da ke yankin suna da kayan kariya da kuma horon da ya dace.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu jami'ai na fargaba kan ko sojojin Amurka a halin yanzu suna da isassun kayan aiki da kuma shirin da ya dace na tunkarar harin makamai masu guba.

Bayanan sirrin na zuwa ne a daidai lokacin da ƙoƙarin diflomasiyya na kawo ƙarshen rikicin Amurka da Iran ya tsaya cik.

Washington da Tehran na ci gaba da saɓani kan batun killace hanyoyi, da sake buɗe mashigar ruwan Hormuz da kuma sharuddan da ake buƙata domin kawo ƙarshen faɗan.

Wata majiya daga yankin ta shaida wa CNN cewa makonni masu zuwa na iya zama masu matuƙar muhimmanci ga tattaunawar sulhu, tana mai gargaɗin cewa masu tsattsauran ra'ayi a Iran ko wasu ɓangarorin da ke adawa da yarjejeniya na iya ƙoƙarin kawo cikas ga ƙoƙarin diflomasiyyar.