Wani bincike da aka yi kwanan nan ya gano cewa kusan rabin dukkan rahotannin kafafen watsa labaran Birtaniya game da Musulmai na ɗauke da wani mataki na nuna son kai.
Binciken da Cibiyar Sanya idanu Kan Kafafen Watsa Labarai (CfMM) ta gudanar ya gano cewa nuna son kai ya yaɗu a faɗin kafafen Watsa labarai na Birtaniya a shekarar 2025, inda kusan kashi 50 cikin ɗari na dukkan labaran suka ƙunshi wani nau'in nuna son kai.
Rahoton ya gano cewa kusan labarai 20,000 daga cikin labarai 40,913 da aka buga a manyan gidajen watsa labarai 30 sun nuna son kai ta wata hanya.
Ya kuma bayyana cewa kashi 70 cikin ɗari na labaran sun haɗa Musulmai ko Musulunci da halaye ko matsaloli marasa kyau.
Rahoton ya bayyana kafofin watsa labarai na masu ra’ayin rikau a matsayin babban tushen nuna son kai ga Musulmai, inda The Spectator ke da mafi yawan labara masu cike da "son kai".
Sauran gidajen watsa labarai da suka fi nuna son kai ga Musulmai sun haɗa da GB News, The Telegraph, Jewish Chronicle, Daily Express, The Sun, Daily Mail da The Times.
"A matsayin babban bincike irin sa da aka taɓa yi a Birtaniya, wannan rahoton ya gabatar da hujjoji masu tayar da hankali game da nuna son kai a tsarin yadda ake nuna Musulmai a cikin jaridun Birtaniya," in ji Rizwana Hamid, darektan CfMM.













