| Hausa
KIMIYYA DA FASAHA
3 minti karatu
Ɗan sama jannatin da ya kamu da rashin lafiya ya sa dole jirgin NASA ya dawo duniya
SpaceX ya jagoranci saukar rokar a yankin Tekun Pacific kusa da San Diego, ƙasa da awanni 11 bayan da 'yan sama janatin suka bar Tashar Sararin Samaniya ta Ƙasa da Ƙasa. ISS.
Ɗan sama jannatin da ya kamu da rashin lafiya ya sa dole jirgin NASA ya dawo duniya
Ɗan sama jannatin da ya kamu da rashin lafiya da ya sa dole jirgin NASA ya dawo duniya / AP

Wani ɗan sama jannati da ya kamu da rashin lafiya ya dawo Duniya tare da wasu mutum uku a ranar Alhamis a cikin wata rokar hukumar NASA da aka ƙra da nufin kwaso marasa lafiya daga sararin samaniya, lamarin da ya kawo ƙarshen aikinsu a tashar sararin samaniya fiye da wata ɗaya kafin lokacin da ya kamata su dawo ya yi, abin da ya zama aikin ceto na lafiya na farko da rokar ta NASA ta yi.

SpaceX ya jagoranci saukar rokar a yankin Tekun Pacific kusa da San Diego, ƙasa da awanni 11 bayan da 'yan sama janatin suka bar Tashar Sararin Samaniya ta Ƙasa da Ƙasa. ISS.

Lamarin yawo ƙarshen wannan bulaguro bagatatan wanda aka fara shi a watan Agusta inda ya bar rokar ta kwasar marasa lafiyatana cigaba da kewaya duniya da mutum ɗaya Ba’amurke da 'yan Rasha biyu a ciki.

NASA da SpaceX sun ce za su yi ƙoƙarin gaggawa wajen ƙaddamar da wata sabuwar tawagar mai mutane huɗu; inda aka shirya harba rokar sama a halin yanzu a tsakiyar Fabrairu.

Zena Cardman da Mike Fincke na NASA sun dawo tare da Kimiya Yui na Japan da Oleg Platonov na Rasha. Jami'ai sun ƙi bayyana sunan ɗan sama jannatin da ba shi da lafiyar ko yin bayani kan abin da ya faru, suna ba da dalilai na kariyar bayanan lafiya.

Ko da yake ɗan sama jannatin yana cikin kwanciyar hankali a cikin rokar, NASA ta so a dawo da shi Duniya da wuri-wuri domin ya samu kulawa ta likita da gwaje-gwajen gano cuta.

Jami'ai sun ce dawowa cikin duniya da sauka a teku ba sa buƙatar wasu canje-canje na musamman ko tanadi, kuma jirgin ruwa na ceton yana da ɗauke da tawagar masana lafiya da aka ajiyewa a cikinsa.

Ba a san nan da nan lokacin da za a tashi daga California zuwa hedkwatarsu a Houston ba. Hakanan ba a tabbatar da dawowar Platonov zuwa Moscow ba.

NASA ta jaddada sau da yawa a cikin makon da ya gabata cewa wannan ba lamarin gaggawa ba ne. Astronaut ɗin ya kamu da rashin lafiya ko ya ji rauni a ranar 7 ga Janairu, wanda ya tilasta wa NASA soke aikin fita waje a washegari da aka shirya ‘yan sama jannati Cardman da Fincke za su yi, kuma a ƙarshe ya haifar da dawowa kafin lokaci.

Wannan shi ne karo na farko da NASA ta dakatar da tafiye-tafiye na sararin sama saboda dalilan rashin lafiya. Rasha ta riga ta yi haka shekaru da dama da suka wuce.

Tashar sararin samaniya ta taɓa yin aiki da 'yan sama jannati uku a baya, wani lokaci ma da biyu kaɗai. NASA ta ce ba za ta iya yin aikin fita waje, ko da don gaggawa ba, har sai isowar tawagar ta gaba, wadda ke da Amurkawa biyu, Faransawa ɗaya da ɗan Rasha ɗaya.

Rumbun Labarai
Gidauniyar Gate da OpenAI sun ƙaddamar da shirin inganta lafiya ta hanyar fasahar AI a Afirka
Duniyar dijital: Yadda annobar son waya da komfuta ke hana yara jin daɗin ƙuruciya da samun kulawa
Jirgin sama jannati mai zagaye sararin samaniya na farko da aka ƙera a Turkiyya zai fara aiki
Butum-butumin NASA ya ɗauki yadda aka yi walƙiya a duniyar Mars a lamarin da ba a taɓa gani ba
Masanin kimiyya na Turkiyya ya jagoranci 'yan sama jannati wajen gano sabbin duniyoyi
An fara baje-kolin fasahar jiragen sama ta TEKNOFEST a Istanbul
Hatsarin da ke tattare da gem din Roblox ga yara ya sa Saudiyya da UAE haramta shi
Hirar Xi da Putin kan tsawon rayuwa har shekara 150: Shin ilimin kimiyya ya kai wannan matakin?
An kai Agushi sararin samaniya ya yi kwana bakwai don yin binciken kimiyya a kansa
Afirka za ta iya zama 'kan gaba a fannin sabunta makamashi': Sakatare Janar na MDD
Iyakar ikon kasashe kan Kirkirarriyar Basira da abin da hakan ke nufi ga tsarin tafiyar da duniya
Grok ta dawo aiki bayan dakatar da ita don bankaɗar da ta yi kan kisan ƙare dangi na Gaza
Kirkirarriyar Basira na ƙoƙarin magana da harsunan Afirka, Ko ƙarshen watsi da harsunan ya zo?
WhatsApp ya rufe shafuka fiye da miliyan 6.8 masu alaƙa da zamba: Meta
Google ya amince tsarin gargaɗinsa ya gaza ceton miliyoyin mutane a girgizar ƙasar Turkiyya a 2023
Masana kimiyya sun ɗauki hoton da ba a saba gani ba na mutuwar taurari a kaunu
Amurka ta sauya wa kayayyakin sojinta wuri, ta rage shiga sansaninta mafi girma a Gabas ta Tsakiya
Meta na tattaunawa da kamfanin Scale AI domin zuba jarin fiye da dala biliyan 10 — rahoto
Masu fafutuka suna son a sauya tsarin TikTok saboda gazawar shafin daga kare yara
Ɓoyayyun duwatsun astiriyod na duniyar Venus za su iya faɗowa duniyarmu - Bincike