Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ƙasarsa za ta soma wata sabuwar tattaunawa da Iran a ranar Litinin, yana mai nuna kyakkyawan fata na iya cim ma yarjejeniya kan buɗe Mashigar Hormuz da kuma "kawar da makaman nukiliyar Iran" nan ba da jimawa ba.
Da yake magana da manema labarai a cikin jirgin Air Force One da ke kan hanyarsa ta zuwa sansanin sojojin haɗin gwiwa na Andrews da ke Maryland, Trump ya ce tattaunawa tsakanin Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Qatar da kuma Iran ta sanya shi soke shirin "babban harin da aka yi niyya kaiwa" a ranar Jumma'a.
"Ba sa son mu yi hakan, kuma a gaskiya, Saudiyya ma ba ta so. Sun yi tunanin cewa za a cim ma yarjejeniya a nan kusa... wadda take da alaƙa da Mashigar Hormuz da kuma kawo ƙarshe shirin makaman nukiliya," in ji shi.
"Manyan ƙasashen uku sun tambaye mu. Iran ma ta yi mana tambayoyi sosai," in ji Trump. "Sun ce muna so a cim ma yarjejeniya."
Da aka tambaye shi ko Iran tana da wa'adi na cim ma yarjejeniya, Trump ya ce babu wani lokaci da aka tsara.
"Za mu gani kawai," in ji shi, yayin da yake jaddada cewa a shirye Amurka take domin yin amfani da ƙarfin soji idan ya zama dole.
"A shirye muke mu tafi duk lokacin da muka so. Zan fi so a cim ma yarjejeniya. Ba na so a kashe mutane saboda mutane suna mutuwa, mutane da yawa suna mutuwa, kuma ba ma son hakan," in ji shi.
Yayin da aka tambaye shi ko wannan harin zai shafi fannin samar da makamashi na Iran, Trump ya ƙi yin ƙarin bayani.

"Tsarin yarjejeniyar da aka amince da ita"
Wannan sabon ci-gaban da aka samu ya biyo bayan soke wani shirin kai hari kan Iran da shugaban Amurka ya sanar, yana mai cewa an amince da tsarin yarjejeniyar, yayin da ya sanya sharaɗi na cim ma yarjejeniya cikin sauri.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce Amurka ta shirya kai hari kan Iran amma Iran da sauran ƙasashen yankin Gabas ta Tsakiya sun nemi a dakata.
Ya ce an amince da tsarin yarjejeniyar kuma zai haɗa da "buɗe Mashigar Hormuz nan-take kuma gabaki ɗaya" da kuma "kawo karshen barazanar nukiliyar Iran."
"Bisa ga wannan buƙatar, na amince, don amfanin DUNIYA a nan gaba, haka kuma, don tsirar da makomar nasara da wadatar Iran, sannan idan za a soke harin, dole a cim ma yarjejeniya cikin sauri,’’in ji Trump.
Ya kuma ce Isra'ila "ta na tare da shi a wannan buƙatar."
Trump ya ƙara da cewa Amurka ta "cika ta batse, sannan a shirye ta ke" ta yi yaƙi da Iran kafin ta yanke matsaya kan dakatar da shirin kai harin.

















