| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Libya ta buƙaci MDD ta tallafa wa ‘yan ci-rani da ‘yan gudun hijira da ke son komawa ƙasashensu
Libya dai na ci gaba da fuskantar matsalar ‘yan ci-rani, inda ƙasashen Tarayyar Turai da ke gabar tekun Mediterrenean ke nuna damuwarsu kan yadda bakin haure ke kwarara ta gabar tekunsu.
00:00
Libya ta buƙaci MDD ta tallafa wa ‘yan ci-rani da ‘yan gudun hijira da ke son komawa ƙasashensu
Tun daga shekarar 2015, hukumar IOM ta taimaka wajen mayar da ‘yan gudun hijira kusan 80,000 daga Libya / Reuters

Ministan harkokin cikin gida na Libya Emad Trabelsi ya bukaci tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Libya (UNSMIL) da ta tallafa wa shirin komawar ‘yan gudun hijira da ‘yan ci-rani da suka nuna sha’awar koma wa kasashensu na asali daga Libya. 

Bukatar hakan ta zo ne a yayin taron da Trabelsi ya yi da wakiliyar MDD ta musamman a Libya Hanna Tetteh da tawagarta wadanda suka kawo ziyara hedkwatar ma’aikatar harkokin cikin gida na kasar da ke birnin Tripoli a ranar Laraba, a cewar sanarwar da ma’aikatar ta fitar.

Sanarwar ta ce taron ya tattauna batutuwan da suka shafi tsaro daban-daban da karin bayanai game da ayyukan ma’aikatar, da kuma dabarun tsaro da nasarorin da ta samu a kasa.

A yayin taron, Trabelsi ya bayyana mumunan illar tasirin yadda ake hijira ba bisa ka'ida ba a kan Libya da kasashen Mediterranean tare da jaddada muhimmancin goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ga kokarin ma'aikatar wajen aiwatar da shirin komawar ‘yan gudun hijirar da ke son komawa gida bisa ga son ransu.

Hanyar hamada

A watan Yulin 2024, Trabelsi ya kiyasta cewa yawan ‘yan gudun hijira a Libya ya wuce mutum miliyan 3, inda ake samun kwararar bakin haure 90,000 zuwa 120,000 da ke shiga kasar duk wata ta hanyar hamada.

Baya ga wannan shiri na Libya, Hukumar Kula da ‘Yan gudun hijira ta Duniya  (IOM) ita ma tana gudanar da shirin mayar da ‘yan gudun hijirar da ke son koma wa gida bisa ga kashin kansu.  

Tun daga shekarar 2015, hukumar IOM ta taimaka wajen mayar da ‘yan gudun hijira kusan 80,000 daga Libya, a cewar kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.

Kasar Libya dai na ci gaba da fuskantar kalubalen ‘yan ci-rani, inda kasashen Tarayyar Turai da ke gabar tekun Mediterrenean ke nuna damuwarsu kan yadda bakin haure ke kwarara zuwa gabar tekunsu.

A halin da ake ciki kuma, mahukuntan Libya sun jaddada cewa, kasar ta kansance  wuri da ake ratsawa ta cikinta ba wai kasa ta asali ba da ‘yan ci-ranin ke tasowa ba, suna masu zargin kasashen Turai da yin sakaci da rawar da suke takawa wajen shawo kan lamarin.

 

 

 

MAJIYA:AA
Rumbun Labarai
Majalisar Dattawan Aljeriya ta amince da buƙatar tura sojoji zuwa Nijar
Gabon ta janye takunkumin amfani da kafafen sada zumunta bayan watanni takwas
Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola
Ana fargabar mutane da dama suna ƙarƙashin ɓaraguzan gini mai hawa 12 da ya rushe a Kenya
Daga Nijeriya zuwa Kenya, mutane na tsawon rai amma ba tare da cikakkiyar lafiya ba
Hamshakiyar attajira ‘yar kasar Mali ta sa sarƙar zinare mai darajar dala miliyan 1.6
Ministocin makamashi na ƙasashen ECOWAS na taro kan ajiyar batura da dokokin kasuwannin lantarki
An saki wasu mata ’yan Turai biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar bayan shafe watanni a tsare
Nijar: Hukumomi sun ɗauki matakan tsaro na gaggawa a Agadez bayan harin da ya kashe mutum 12
Kenya ta kulla yarjejeniyar $160m ta kiyaye muhalli, da goyon bayan magadan attajiran Amurka
Ghana na shirin tunkarar Ebola bayan ɓullar cutar a Kongo DRC da Kenya da Nijeriya
Kasashe da kungiyoyin kasa da kasa na taro a Geneva don habaka kokarin samar da zaman lafiya a Sudan
Darajar kuɗin Sudan ta faɗi, inda ake canza dala ɗaya an kan fam 10,000 na ƙasar
Uganda ta musanta samun  Ebola a ƙasarta bayan wata fasinja 'yar Nijeriya ta nuna alamun cutar
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da man fetur da gas zuwa ƙasashen waje
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai
Ghana ta ware cedi 35m don farfaɗo da gandun dajin da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida bacta ɓata