Iran ta ce tana ci gaba da musayar saƙonni da Amurka, amma a halin yanzu babu yanayin da ya dace a sake fara tattaunawa saboda Washington ta kawo cikas ga diflomasiyya ta hanyar ayyukanta na soji, in ji kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baqaei.
A wata hira da gidan talabijin na ORF na ƙasar Austria, Baqaei ya ce babban abin da Iran ta sa a gaba a yanzu shi ne kare ikon ƙasarta, ba shiga tattaunawa ba.
"Muna ci gaba da musayar saƙonni, amma abin da muka fi mayar da hankali a kai yanzu shi ne kare ikon Iran, martabar ƙasarta da kuma al'ummarta," in ji shi.
Baqaei ya zargi Washington da ci gaba da kawo cikas ga diflomasiyya, yana mai cewa matakan da Amurka ta ɗauka sun lalata yanayin da ake buƙata domin gudanar da tattaunawa, kuma sun saɓa wa yarjejeniyoyin da aka cim ma da Tehran a baya.

Ya bayyana hare-haren baya bayan nan na Amurka a matsayin ci gaba da "yaƙi ba bisa ƙa'ida ba" kan Iran, yana mai cewa hakan ya nuna Washington ta gaza cika alƙawuran da ta ɗauka.
Rikicin yankin
Dangane da Mashigar Ruwa ta Hormuz, Baqaei ya ce Iran ta cika nauyin da ya rataya a wuyanta na tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa na ƙasa da ƙasa, amma ba za ta bari a yi amfani da wannan muhimmiyar mashigar ruwa wajen barazana ga tsaron ƙasar ba.
Ya kuma ɗora alhakin ƙara ta'azzarar rikicin yankin kan Amurka da Isra'ila, yana mai cewa ayyukansu na soji sun dagula yanayin tsaro a yankin.
Da yake magana kan yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015, Baqaei ya ce ƙasashen Turai sun gaza cika alƙawurran da suka ɗauka bayan Amurka ta fice daga yarjejeniyar, yana mai cewa suna "bin Iran babban bashi" saboda sun yi watsi da nauyin da ke kansu.
Rikici tsakanin Amurka da Iran ya ƙara tsananta a cikin makonnin baya-bayan nan, inda Amurka ta kai hare-hare kan Iran, yayin da Tehran ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da kayan aikinsu a ƙasashe da dama na yankin, ciki har da Bahrain, Jordan da Kuwait.
A ranar 8 ga Yuli, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa takardar fahimtar juna da aka saka wa hannu tsakanin Amurka da Iran ta "ƙare", yana zargin Tehran da karya yarjejeniyar.
Sanarwar ta biyo bayan hare-haren da aka kai kan tankokin mai uku a Mashigar Hormuz da kuma sake samun saɓani kan dokokin zirga-zirgar jiragen ruwa a wannan muhimmiyar mashigar ruwa.
Washington ta yi kira da a ba da damar zirga-zirgar jiragen ruwa ba tare da wani takunkumi ba ta Mashigar Hormuz, yayin da Tehran ke dage kan cewa jiragen ruwa su rika bi ta wata hanya da ke kusa da gabar tekunta ƙarƙashin tsarin zirga-zirgar ruwa da Iran ke gudanarwa.
Jaridar Axios a ranar Asabar, ta ruwaito majiyoyi da suke da masaniya game da batun, kan cewa Trump ya umarci sojojin Amurka da kada su ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Iran, lamarin da ya kawo ƙarshen kusan makonni biyu na hare-haren yau da kullum.


















