| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Sojojin Burkina Faso sun ce sun kashe 'yanta'adda fiye da 400 a wani hari da suka daƙile
Gwamnatin Burkina Faso ta zargi Faransa da ɗaukar nauyin 'yanta'addan inda ta ce 'yanta'addan sun kai mata harin ne kwana guda bayan ta sanar da yanke duk wata hulɗa ta diflomasiyya da Faransa.
Sojojin Burkina Faso sun ce sun kashe 'yanta'adda fiye da 400 a wani hari da suka daƙile
Sojojin sun kuma bayar da rahoton mutuwar jami'ansu guda uku yayin fafatawar, ciki har da biyu a Solhan da ɗaya a Gayeri.

Sojojin Burkina Faso a ranar Laraba sun ce sun daƙile hare-haren da ƙungiyoyin ‘yanta’adda suka kai wasu sansanonin soji a ranar 30 ga Yuni, inda aka kashe fiye da mahara 400.

Sojojin sun daƙile harin ne bayan samun taimako daga jiragen sama.

A cikin wata sanarwa da Hedkwatar Sojin Burkina Faso ta fitar ranar Laraba da daddare, ta ce ‘yanta’addan sun kai hare-hare kan sansanonin soji da kuma jami’an sa-kai don kare ƙasa a ƙauyukan Gayeri da ke yankin Sirba, da Solhan da Sebba a yankin Liptako.

A cewar rundunar, sojojin ƙasa, tare da goyon bayan jiragen sama, sun mayar da martani nan-take ga hare-haren.

Sun ce “hare-hare ta sama da ta ƙasa sun yi sanadin kashe ‘yanta’adda fiye da 400” da ba su damar ƙwato kayayyakin yaƙi masu yawa, ciki har da babura fiye da 250, makamai 353 na nau'o'i daban-daban, harsasai da kayayyakin sadarwa.

Masu AlakaTRT Afrika - Burkina Faso ta kawo ƙarshen dangantakar diflomasiyya da Faransa

Sojojin sun kuma bayar da rahoton mutuwar jami'ansu guda uku yayin fafatawar, ciki har da biyu a Solhan da ɗaya a Gayeri.

“Ayyukan tsaro na ci gaba kuma suna ƙaruwa domin bin diddigin waɗanda suka gudu da tabbatar da tsaron lafiyar 'yan ƙasa,” in ji rundunar.

Ta roƙi mazauna su haɗa gwiwa da jami'an tsaro, su bi umarnin tsaro, su kuma ba da rahoton mutanen da ake da shakku a kansu.

Sanarwar ta alaƙanta hare-haren da yanke hulɗar diflomasiyya da Burkina Faso ta sanar da Faransa inda aka kai harin kwana guda bayan sanarwar.

Burkina Faso ta kuma zargi ƙasar Faransa da bayar da goyon baya ga ƙungiyoyin ‘yanbindigar.

Rumbun Labarai
Afirka ta Kudu ta mai da fiye da mutum 25000 kasashensu kafin wa'adin 30 ga Yuni na masu ƙyamar baƙi
Yadda abinci ke yin kisan mummuƙe a Afirka
Burkina Faso ta kawo ƙarshen dangantakar diflomasiyya da Faransa
Fiye da mutum 1,400 sun tsere daga jihar North Darfur ta Sudan a yini ɗaya yayin da ake zafafa yaƙi
Nijeriya da ƙasashe 4 sun ƙaddamar da sabuwar hukuma kan hanyar Abidjan zuwa Lagos ta $16bn
Nijar ta gabatar da takardar buƙatar ficewa daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya, ICC
An ci gaba da amfani da cin zarafin jinsi a matsayin makamin yaƙi a Sudan: MDD
Manyan Jami’o’in Afirka: Afirka ta Kudu ce ke kan gaba a awon matsayi na baya bayan nan
Sudan na son Turkiyya ta jawo hankalin duniya dangane da yaƙin basasar da ake yi a ƙasar
Nijar ta gindaya wa Benin sharruɗa kan sake buɗe iyakar kasashen biyu
MDD ta yi gargadi kan barazanar 'babban zalunci kan bil'adama' da ke tafe a birnin El-Obeid na Sudan
Cutar Ebola: Ma'aikatan lafiya 17 sun rasu yayin da cutar ke 'yaɗuwa cikin sauri'
Aljeriya da Benin sun nuna goyon baya ga Nijar bayan hari kan filin jiragen sama
Ghana ta nemi a biya diyyar cinikin bayi
Harin da aka kai filin jirgin saman Nijar ya kashe jami'an tsaro 11, in ji gwamnati
Taƙaddama ta ɓarke tsakanin Chadi da Kamaru kan wani aikin layin dogo
An ji ƙarar harbe-harbe a kusa da babban filin jirgin sama na Nijar da ke Yamai
An kama mutum da kunamu 150 ɓoye a tufafinsa a filin jirgin sama na Afirka ta Kudu
Somaliya ta karɓi kayan aiki na zamani daga Turkiyya don inganta harkar noma
Mutum 28 sun mutu a Ethiopia bayan wata bas ta faɗa a kwazazzaɓo