| Hausa
DUNIYA
1 minti karatu
Trump: Amurka na duba yiwuwar 'kammala' hare-haren soji kan Iran
Trump ya ce sauran ƙasashe da ke amfanin da Mashigin Hormuz ne suka kamata su ba shi kariya, ba Amurka ba.
Trump: Amurka na duba yiwuwar 'kammala' hare-haren soji kan Iran
Trump ya tattauna da manema labarai kafin ya shiga jirgin Marine One daga Fadar White House, ranar 20 ga Maris, 2026 / AP
21 Maris 2026

Shugaban Amurka Donald Trump ranar Jumma’a ya ce yana duba yiwuwar “kammala” hare-haren soji da ake kai wa Iran sannan ya ƙara da cewa sauran ƙasashe ne suka kamata su “bayar da kariya tare da sanya ido” kan Mashigin Hormuz saboda muhimmancinsa.

"Mun kusa cim ma muradunmu don haka muna duba yiwuwar kammala ayyukan da gwarazan sojojinmu suke yi a Gabas ta Tsakiya game da Gwamnatin Ta’addanci ta Iran," a cewar Trump a wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta na Truth Social.

Masu AlakaTRT Afrika - Mashigar Hormuz: Hanyar ruwan da za ta iya girgiza tattalin arzikin duniya

"Ƙasashen da ke amfani da Mashigin Hormuz su ne suka kamata su ba shi kariya tare da sanya idanu a kansa -- Amurka ba za ta yi bat!" in ji shi.

Lamura sun dagule a yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare a Iran ranar 28 ga Fabrairu. Rahotanni sun ce hare-haren sun kashe aƙalla mutum 1,300, cikinsu har da ƙananan yara mata ‘yan makarantar firamare fiye da 150.

Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan Isra’ila da kuma kayayyakin Amurka da ke ƙasashen Larabawa, abin da ya ƙara yamutsa yaƙin.

Rumbun Labarai
Tsarin kiwon lafiya a Gabas ta Tsakiya na fuskantar barazana yayin da rikici ke ƙara muni: WHO
Kusan rabin rahotannin kafafen watsa labaran Birtaniya kan Musulmi na dauke da nuna wariya
Mashigar Hormuz: Hanyar ruwan da za ta iya girgiza tattalin arzikin duniya
Dalilai huɗu da suka sa matasan Afirka suka fi lafiyar ƙwaƙwalwa a duniya
Musulmai a Turkiyya, Oman, Singapore, da Australia za su fara azumin Ramadan a ranar Alhamis
'Babu wani takamaiman abin da aka cim ma' a ganawar Trump da Netanyahu a kan Iran
An ci tarar ƙananan hukumomi 10 a Holland kan binciken al'ummomin Musulmai ba tare da saninsu ba
Trevor Noah: Trump ya yi barazanar maka mai gabatarwa a Gasar Grammy a Kotu
Saudiyya da Isra'ila za su Amurka don tattaunawa yayin da Trump ke tura jiragen yaƙi na ruwa Iran
WHO: Amurka ta fita daga Hukumar Lafiya ta Duniya bayan shekara 78
Masana kimiyya sun gano zanen shacin hannu 'mai shekara 67,800' a wani kogo a Indonesia
Ministan Wajen Saudiyya da takwarorinsa na Iran, Oman da Qatar sun tattauna kan zaman lafiyar yanki
Amurka ta dakatar da ba da bizar masu ƙaura ga 'yan Nijeriya da wasu ƙasashe 74
Wani sanatan Amurka ya yi gargaɗi kan ƙaruwar ƙyamar Musulunci da ƙin jinin Larabawa
Trump ya saka harajin kashi 25 kan ƙasashen da ke kasuwanci da Iran
An katse intanet da wayoyin hannu a Iran
Matar shugaban Turkiyya ta gana da shugaban UNRWA kan shirin buɗe ofis a Ankara
Sanatocin Republican 5 sun bi sahun 'yan Democrat don neman sake duba ikon yaki na Trump a Venezuela
An kashe ɗansanda a kusa da Tehran yayin da zanga-zanga kan matsin rayuwa ta mamaye ƙasar Iran
Erdogan da Anwar na son ƙarfafa alaƙar Turkiyya da Malaysia tare da fifita fannin tsaro