| Hausa
AFIRKA
5 MINTI KARATU
Ayyuka 14 da Shugaba Buhari zai kaddamar a makon karshe na mulkinsa
Duk da cewa 'yan kwanaki ne suka rage masa a kan mulki, Shugaba Buhari ya shirya kaddamar da wasu jerin ayyuka 14 kafin ya mika mulkin a farkon mako mai zuwa.
Ayyuka 14 da Shugaba Buhari zai kaddamar a makon karshe na mulkinsa
Shugaba Buharin zai kaddamar da ayyuka 14 a fadin kasar /Hoto: Presidency / Others

Makon gobe ne zai kasance na karshe a mulkin Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari bayan shafe shekara takwas a kan mulki, inda zai mika mulki ga sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Sai dai duk da cewa 'yan kwanaki ne suka rage masa a kan mulki, Shugaba Buhari ya shirya kaddamar da wasu jerin ayyuka 14 kafin ya mika mulkin a farkon mako mai zuwa.

Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan kafofin sada zumunta na zamani, Bashir Ahmad ne ya bayyana jerin ayyukan da shugaban kasar zai kaddamar a wannan makon, a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

Ayyukan da za a kaddamar su ne:

  • Matatar Mai ta Dangote da ke Legas

  • Gadar Loko zuwa Oweto da ke jihar Nasarawa

  • Gadar Second Niger Bridge da ta hada jihohin Delta da Anambra

  • Gadar Ikom a jihar Cross River

  • Hanyar Kaduna zuwa Kano (wani bangare na aikin titin Abuja zuwa Kano)

  • Sakatariyar Tarayya a jihar Zamfara

  • Sakatariyar Tarayya a jihar Anambra

  • Sakatariyar Tarayya a jihar Bayelsa

  • Wurin hada taragon jirgin kasa a jihar Ogun

  • Cibiyar nazarin ayyukan majalisa da dimokradiyya ta kasa a Abuja

  • Sabon wurin saukar fasinjoji a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a jihar Kano

  • Wasu ayyuka a Kwalejin Koyon Tukin Jirgin Saman a Zaria

  • Filin jirgin saman jihar Ebonyi a Ebonyi

  • Sabuwar hedikwatar hukumar kwastam din kasar a Abuja.

Me ya sa shugaban ke kaddamar da ayyukan dab da saukarsa?

Wannan ita ce tambayar da watakila mutane da dama suke yi wa kansu.

TRT Afrika ta tuntubi wani masanin harkokin siyasa a Jami'ar Abuja, Dr Abubakar Kari, wanda ya ce wannan ba sabon abu ba ne ga shugabannin da ke shirin barin gado.

"A duk lokacin da wa'adin wata gwamnati ya karato ko ya zo karshe, to za ta yi kokarin ta tabbatar da cewa ta fada wa duniya cewa ayyuka kaza da kaza da wannan da wancan a lokacinta aka yi.

"Za ka ga ana ta hanzarin kaddamar da ayyukan da aka faro wasunsu ma ko ba a karasa su ba," in ji shi.

Ya kara da cewa: "Kawai suna so ne tarihi ya tuna cewa su ne suka fara wannan aiki ko su ne suka kammala shi.

"Saboda a tunaninsu idan ba su yi haka ba, wadanda suka zo bayansu, ko dai za su yi ikirarin cewa su ne suka yi aikin ko kuma ba za su fada wa duniya sunan ainihin wanda ya yi aikin ba."

Su ma 'yan Nijeriya ba a bar su a baya ba wajen tofa tasu kan wannan lamari, inda suka dinga yin tsokaci a kasan sakonni da Bashir Ahmad ya wallafa.

Sai dai a yayin da wasu ke yabo da jinjina, wasu kushe suka dinga yi kan wannan labari.

Salihu Tanko @salihutanko11 ya ce: "Ba a taba ganin irin wannan ba a tarihin Nijeriya, tarihi ba zai manta da Shugaba Buhari ba saboda manyan ayyukan ci gaba da ya yi. Na jinjina maka."

Shi kuwa Dammy @oyeladedami cewa ya yi: "Ya kaddamar da ayyukan da suka fara aiki nan take, amma ba ayyukan bogi ba, kamar tashar Baro."

"Ya kasa gina matatar mai a tsawon shekara takwas. Yanzu ya kaddamar da Matatar Man Dangote. Wai shin ba ku ji kunya ba," in ji IGWE @igwe_manuel.

SAAD @mahmudchiroma yaba wa shugaban ya yi, inda ya ce: "Shugaban da ba a taba samun irinsa ba… Gwarzo, uban sabuwar Najeriya…kowa ya kamata ya jinjina maka."

A karshe akwai ra'ayin Ahmad N.M @ahmadrufai wanda shi ya kalubalanci Bashir Ahmad ne, inda ya ce masa "Me ya sa ba ka saka har da shirin dawo da kamfanin sufurin jirgin saman Nigeria Airways ba?"

MAJIYA:TRT Afrika
Rumbun Labarai
Ana hasashen kuɗin da Angola za ta kashe kan tallafin fetur a 2026 zai kai dala biliyan hudu
Shugaban Masar Al-Sisi ya ce zai sauka daga mulki a 2030 ba tare da tsawaita wa'adin mulkinsa ba
Africa CDC ta ce ba a san yadda aka kashe fiye da dala miliyan 700 na kuɗin yaƙi da Ebola ba
Ya zama dole Afirka ta daina tambayar ‘me duniya za ta sayar mana’ kawai
Ghana ta ware cedi 35m don farfaɗo da gandun dajin da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida bacta ɓata
Kenya ta ƙara farashin man fetur da kashi 6 cikin 100 sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya
Ghana ta kama mutum 19 kan zargin laifukan intanet tare da gano damfarar dala miliyan 8.3
Nijar ta ayyana mummunan haɗarin muhalli bayan malalar mai
Gwamnatin Nijar ta kafa kwamitin magance ƙaranci da basussuka a ɓangaren man fetur
Aljeriya ta kama ‘yan Maroko 61 bisa zargin kitsa mata zagon-ƙasa
An miƙa wa 'yan kwangila ayyukan fara gina azuzuwa 357 a jihar Dosso ta Nijar
Gwamnatin Nijar ta yi watsi da buƙatar ƙarin farashin man fetur a ƙasar
MƊD: An raba mutane miliyan huɗu da gidajensu a Burkina Faso da Mali da Nijar
Sojoji na cikin mutum 71 da aka kashe a Sudan ta Kudu bayan mummunar arangama
Faransa ta kori jami’an leƙen asirin Nijar biyu daga ƙasarta
'Yar Afirka ta Kudu Navi Pillay ta ci kyautar Nobel ta Zaman Lafiya ta shekarar 2026
Rikicin wakilci a yanki: Me ke ta'azzara rikicin Ethiopia-Eritrea?
Haɗuran mota sun yi sanadin mutuwar mutum 2,151 a Ghana cikin watanni tara - Rahoton MTTD
Ethiopia ta nemi a janye dakarun Eritrea 'nan-take' daga ƙasarta
Ghana da FBI sun kama mutum 130 da ke da alaƙa da zambar $10m