| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Ethiopia ta nemi a janye dakarun Eritrea 'nan-take' daga ƙasarta
Kasancewar dakarun Eritrea a yankin Tigray da ke arewacin ƙasar Ethiopia na sanya fargabar yiwuwar rikicin cikin gida da ka iya faɗaɗa zuwa yaƙin yanki.
Ethiopia ta nemi a janye dakarun Eritrea 'nan-take' daga ƙasarta
Yaƙi ya ɓarke tsakanin 'yantawaye na Tigray People's Liberation Front (TPLF) da dakarun Tarrayar Ethiopia ranar 23 ga watan Satumba.

Gwamnatin Ethiopia ta yi kira a janye dakarun Eritrea nan-take daga ƙasarta.

Ministan harkokin waje Gedion Timothewos ne ya yi kiran a lokacin wata ganawa da mataimakiyar sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) Amina J. Mohammed, in ji wani saƙon da ministan ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis.

Timothewos ya jaddada "buƙatar gaggawa ta martanin ƙa’aida na MƊD" tare da "sake jaddada ‘yancin Ethiopia na kare ‘yancin kanta da kuma ‘yancin ƙasarta bisa dokokin ƙasa da ƙasa".

Ofishin MƊD a Ethiopia ya tabbatar da ganawar, yana mai cewa Amina Mohammed ta yi "tattaunawa mai fa’ida" da Timothewos game da abubuwan da ke faruwa a ƙasar da ma yankin gaba ɗaya.

Mutunta ‘yancin kai

"Ta jaddada buƙatar da ke akwai ta mutunta ‘yancin kai da ikon ƙasar Ethiopia da kuma kare zaman lafiyar ƙasar," kamar yadda ofishin ya bayyana a wani saƙo da ya wallafa a shafin X.

Yaƙi ya ɓarke ne tsakanin ƙungiyar ‘yan tawaye TPLF da dakarun Tarayyar Ethiopia ranar 23 ga watan Satumba, lamarin da ya sanya fargaba ta yiwuwar komawa yaƙin basasar shekarar 2020 zuwa 2022.

Dakarun Eritrea sun shiga yankin Tigray na arewacin Ethiopia, kamar yadda majiyoyi suka bayyana ranar Laraba, lamarin da ke barazanar sauya rikicin cikin gidan zuwa yaƙin yanki mai faɗi.

Ethiopia ta yi zargin cewa Eritrea tana goyon bayan ‘yantawayen ne, kuma ƙasashe biyu maƙwabtan juna sun yanke hulɗar diflomasiyya a makon jiya.