| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Aljeriya ta kama ‘yan Maroko 61 bisa zargin kitsa mata zagon-ƙasa
Hukumomi sun ce waɗanda ake zargin sun shiga Aljeriya ne ta hanyar duwatsu daga ƙasar Tunisiya mai maƙwabtaka.
Aljeriya ta kama ‘yan Maroko 61 bisa zargin kitsa mata zagon-ƙasa
Dakarun Aljeriya na musamman sun kama mutum 61, ciki har da wani stohon sojan Maroko.

Hukumomin Aljeriya sun sanar da kama ‘yan ƙasar Maroko 61 a farkon wannan watan bisa zargin shirya ayyukan zagon ƙasa da nufin kawo cikas ga tsaro da zaman lafiyar ƙasar.

A cikin wata sanarwa da kafafen yaɗa labaran Aljeriya suka wallafa ranar Lahadi, Hukumar Tsaron Ƙasa (DGSN) ta ce waɗanda ake zargin suna cikin wata “ƙungiyar masu aikata laifuka ta Maroko”, amma ba ta bayyana cikakken bayani kan ayyukan da ake zargin sun shirya ba.

A cewar hukumar, mutanen 61 ɗin, ciki har da wani tsohon soja daga Maroko, ana zargin suna shirya ayyukan ɓarna da nufin kawo cikas ga tsaro da zaman lafiyar Aljeriya.

Hukumar ta ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun shiga Aljeriya ne ta hanyar yankunan duwatsu daga ƙasar Tunisiya mai maƙwabtaka.

Tsamin dangantakar diflomasiyya

Dangantaka tsakanin Aljeriya da Maroko ta daɗe tana cikin tsami, inda aka rufe iyakar ƙasashen biyu tun shekarar 1994. A shekarar 2021, Aljeriya ta sanar da yanke alaƙar diflomasiyya da Maroko.

Ƙasashen biyu sun daɗe suna saɓani kan batun yankin Yammacin Sahara.

Yankin, wanda a baya yake ƙarƙashin mulkin mallakar Sifaniya, ya kasance wani yanki da ake takaddama a kansa tun bayan ficewar Sifaniya a shekarar 1975.

Majalisar Ɗinkin Duniya tana ɗaukar Yammacin Sahara a matsayin yankin da har yanzu ba a kammala batun ‘yancin kansa ba.

Maroko na kallon Yammacin Sahara a matsayin wani ɓangare na ƙasarta, yayin da Aljeriya ke goyon bayan ƙungiyar Polisario Front, wadda ke fafutukar neman ‘yancin kan yankin.