Wata majiya ta diflomasiyya ta ce Faransa ta ayyana wasu jami’an leƙen asirin Nijar guda biyu da ke aiki a ofishin jakadancin ƙasar da ke Paris a matsayin mutanen da ba a so a ƙasar, lamarin da ya tilasta musu barin Faransa a ranar Jumma’a.
Majiyar ta tabbatar da rahoton jaridar Le Monde, inda ta bayyana cewa an ayyana jami’an ofishin jakadancin Nijar guda biyun a matsayin mutanen da ba a so a ranar 16 ga Satumba, kuma sun bar ƙasar Faransa.
Majiyar ta ƙara da cewa, “Jami’an leƙen asirin Nijar ne guda biyu waɗanda babu wani dalilin ci gaba da zamansu a Faransa, ganin cewa babu haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.”
Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, wanda ya hambarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum, Nijar ke ƙarƙashin mulkin gwamnatin soji. Sojojin sun tsare Bazoum tun daga lokacin.
Gwamnatin mulkin sojin ta juya wa ƙasashen Yamma baya, musamman Faransa, wadda ta taɓa yi wa Nijar mulkin mallaka, inda ta karkata zuwa ƙulla kusancin hulɗa da Rasha yayin da take fuskantar matsalar hare-haren masu tsattsauran ra’ayin addini da suka daɗe suna addabar ƙasar.
A watan Disamban 2023, Faransa ta rufe ofishin jakadancinta da ke Yamai, babban birnin Nijar, har abada, tana mai cewa ofishin ba zai iya gudanar da aikinsa yadda ya kamata ba saboda takunkumin da gwamnatin sojin ta kakaba.
Sai dai ofishin jakadancin Nijar da ke Paris ya ci gaba da aiki duk da tsamin dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.






















