| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
1 minti karatu
Masu aikin Umrah biyu sun rasu, 25 sun jikkata bayan bas ɗauke da 'yan ƙasar Masar ta yi hatsari
Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta ce bas ɗin, wadda ke ɗauke da mahajjata ’yan ƙasar Masar 47, tana kan hanya daga Madina zuwa Makkah lokacin da hatsarin ya afku.
Masu aikin Umrah biyu sun rasu, 25 sun jikkata bayan bas ɗauke da 'yan ƙasar Masar ta yi hatsari
Hukumomin Saudiyya ba su fitar da wani bayani kan hatsarin nan take ba.

Masu yin Umrah ’yan ƙasar Masar biyu sun rasu, yayin da wasu 25 suka jikkata a wani hatsarin bas da ya afku kusa da birnin Al-Jumum na Saudiyya, kimanin mil 17 daga Makkah, kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta sanar a ranar Lahadi.

Ma’aikatar ta ce bas ɗin, wadda ke ɗauke da mahajjata ’yan ƙasar Masar 47, tana kan hanya daga Madina zuwa Makkah lokacin da hatsarin ya afku a yammacin ranar Asabar.

A cewar sanarwar, mutane 25 sun samu raunuka, inda wasu raunukan su da sauƙi wasu kuma matsakaici, ciki har da mutum bakwai da aka kwantar a sashen kulawa na musamman (ICU).

Sauran mahajjatan sun samu kulawar lafiya kuma aka sallame su daga asibiti kafin a kai su otal-otal ɗin da aka tanadar musu a Makkah.

Hukumomin Saudiyya ba su fitar da wani bayani kan hatsarin nan take ba.

Umrah ibada ce wadda Musulmi ke zuwa Makkah domin ziyartar Ka’aba da gudanar da wasu ibadu na bautar Allah da kuma tsarkake kai.