Ministan nan na Isra’ila wanda ya yi ƙaurin-suna wurin tsattsauran ra’ayi kuma shugaban jam’iyyar Jewish Power, Itamar Ben-Gvir, ya gabatar da wani shirin korar Falasɗinawa miliyan 1.86 daga Gaza da aka killace cikin shekaru bakwai, a ƙarƙashin abin da ya kira “ƙaura bisa son rai”, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na Isra’ila suka ruwaito.
Ben-Gvir ya gabatar da shirin, wanda aka kira “Disengagement 710”, a wani taron manema labarai a ranar Alhamis, a matsayin wani ɓangare na yaƙin neman zaɓensa, bayan jaridar Yedioth Ahronoth ta wallafa bayanan shirin.
Jaridar ta ce shirin ya ƙunshi kafa wata ma’aikata ta musamman da za ta aiwatar da aikin tare da samar da kuɗaɗen “tallafin karɓar baƙi” ga ƙasashen da za su karɓi Falasɗinawan.
A yayin gabatar da shirin, Ben-Gvir ya yi iƙirarin cewa akwai ƙasashe da “a shirye suke su karɓi” Falasɗinawa, sannan ya ce “adadi mai yawa na son ƙaura”.
Sai dai Yedioth Ahronoth ta ce a halin yanzu ba a san wata ƙasa da ta amince da karɓar dimbin Falasɗinawa daga Gaza ba.
Rahoton ya ce shirin na da burin korar Falasɗinawa 250,000 a shekarar farko, miliyan 1.11 cikin shekaru uku, sannan kusan miliyan 1.86 cikin shekaru bakwai.
Ya ƙara da cewa Ben-Gvir na shirin mayar da wannan shiri wani babban ɓangare na yaƙin neman zaɓensa, bayan da ya shafe “watanni yana aiki a kansa”.
Jaridar Yedioth Ahronoth ta ce jam’iyyarsa ta Jewish Power ita ma na shirin mayar da amincewa da shirin a matsayin wani muhimmin sharadi a duk wata tattaunawa da za a yi domin shiga gwamnati mai zuwa.
Shirin ya ƙunshi samar da ƙasar da za ta karɓi kowane mutum ko iyali da zai bar Gaza, tare da samar musu da matsayin doka, takardun shaida, biza, kuɗin tafiya da kuma matsugunin farko.
“Ma’aikatar ƙaura”
A cewar rahoton, shirin ya ginu ne kan ƙa’idoji 12, ciki har da abin da ya kira “barin Gaza bisa son rai”, da kuma sharadin cewa “babu wanda zai bar Gaza ba tare da wata ƙasa da ta shirya karɓarsa tare da ba shi cikakken matsayin doka ba”.
Shirin ya kuma ba da shawarar bayar da “kuɗaɗe” ga ƙasashe da hukumomin da za su shiga aikin karɓar mutanen da za su bar Gaza, bisa la’akari da “aikinsu, tantance tsaron kowane mutum da kuma manufofin aiwatar da shirin na kowace shekara”.
Ya kuma buƙaci a samar da “rahotannin kowane wata kan adadin waɗanda suka nemi ƙaura, waɗanda aka amince da su da kuma waɗanda suka bar Gaza”, da kuma “kuɗaɗen da aka kashe da kuma matakin da waɗanda suka bar Gaza suka samu damar shiga cikin al’ummomin ƙasashen da suka je”.
Shirin zai buƙaci Isra’ila ta fara saka dala biliyan 3.3 domin kafa shi da kuma fara aiwatar da shi.
Haka kuma, shirin ya tanadi tsarin samar da kuɗaɗen Isra’ila har dala biliyan 16.6, matuƙar an samu sa hannun ƙasashen duniya da kuma yarjejeniyoyi da ƙasashen da za su karɓi mutanen.
Ben-Gvir ya buƙaci a kafa wata “ma’aikatar ƙaura”, yana mai cewa za ta kasance da minista da kuma wani jami’i na musamman da zai kula da aikin.
A halin yanzu, kusan Falasɗinawa miliyan 2.13 ne ke zaune a Gaza da aka killace.
Isra’ila, wadda ta mamaye kashi 70 cikin 100 na Gaza, ta kashe sama da Falasɗinawa 73,000, galibinsu mata da yara, tare da jikkata fiye da 174,000 tun bayan fara yaƙin da ta kai a Gaza a watan Oktoban 2023.
Ta mayar da mafi yawan yankin da aka killace zuwa kufai, tare da raba kusan daukacin al’ummar Gaza da matsugunansu.
Masu nazari sun yi kiyasin cewa adadin mutanen da suka mutu a zahiri sakamakon yaƙin Isra’ila a Gaza na iya zama mafi girma sosai fiye da alkaluman hukuma, inda adadin zai iya kaiwa 200,000.


















