| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Erdogan ya yaba wa taron COP31 da Turkiyya ta karɓi baƙuncinsa a matsayin 'mafi nasara' a tarihi
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce an fara jin ƙarar sawun wata "babbar Turkiyya mai ƙarfi" ba wai a yankin kaɗai ba har ma da faɗin duniya.
Erdogan ya yaba wa taron COP31 da Turkiyya ta karɓi baƙuncinsa a matsayin 'mafi nasara' a tarihi
Erdogan na gabatar da jawabi a taron ɓangaren matasa na jam'iyyar AK Party a Cibiyar Taron jam'iyyar a Ankara, 16 ga Nuwamban 2026. / َAA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yaba wa taron yanayi na COP31 da Turkiyya ta karɓi baƙuncinsa, yana mai cewa taron ya kasance "mafi nasara kawo yanzu a fannin tsari da samun masu zuwa."

Erdogan ya yi kalaman ne a wani jawabin da ya yi ga mambobin reshen matasa na jam’iyyar Justice and Development (AK) Party a babban birnin ƙasar, Ankara, ranar Litinin.

Da yake ishara ga wani muhimmin taro da Turkiyya ta karɓi baƙuncinsa kuma, Erdogan ya ce taron shugabanni na ƙawancen tsaro na NATO, da aka yi a Ankara a cikin watan Yuli, na ci gaba da samun wani tasiri mai ɗorewa.

“Tasirin taron abu ne da har yanzu ana jin sa. A halin yanzu ana jin ƙarar tafiyar sawun babbar Turkiyya mai ƙarfi ba wai a yankinmu kaɗai ba, har ma a faɗin duniya,” in ji shi.

Yayin da yake jaddada tasirin Turkiyya da ke ƙaruwa a duniya, Erdogan ya ce ƙasar tana ƙara kasancewa ƙasar da duniya ta mayar da hankali kanta inda tsare-tsarenta na cikin gida da na ƙetare ke jan hankali daga sassan duniya.

"Yayin da wani sabon tsarin duniya ke bayyana, ku ne za ku mayar da mafarkinmu na Turkiyya a matsayin ‘ƙasar tsakiya’ gaskiya," kamar yadda Erdogan ya shaida wa matasan da ke halartar taron.