Firaministar Bangladesh Sheikh Hasina ta sauka daga muƙaminta, a cewar babban hafsan sojin ƙasar, yana mai cewa gwamnatin riƙon ƙwarya za ta jagoranci ƙasar har lokacin da za a yi zaɓe.
Sai dai ba a san inda take ba ko da yake rahotanni na cewa ta tsere daga ƙasar bayan masu zanga-zanga sun kutsa kai cikin gidanta.
Babban hafsan sojojin ƙasar Waker-Uz-Zaman ya roƙi masu zanga-zangar su koma gida domin ƙyale sojoji mu maoido da zaman lafiya.
Wannan mataki ya kawo ƙarshen shekara 15 na jam'iyyar Awami League, wadda ita ce jam'iyyar mutumin daya kafa ƙasar.
Tun da farko rahotanni sun ce Hasina, mai shekara 76, tare da 'yar'uwarta, sun fice daga Dhaka a yayin da zanga-zanga ta yi ƙamari.
Rahotannin sun ce da farko ta tafi a jerin gwanon motocinta amma daga bisani an "ɗauke ta jirgin helikwafta."
Ɗaruruwan masu zanga-zanga cike da murna sun riƙa ɗaga tutoci, inda suka hau kan tituna ranar Litinin da safe kafin su kutsa cikin gidan gwamnati inda Hasina take.