Mutane biyu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu mutum biyar suka jikkata sakamakon harbin da aka yi musu a birnin Timbuktu da ke arewacin Mali, kamar yadda rundunar sojin kasar ta sanar.
Hakan na faruwa ne bayan wata daya da rabi da masu tayar da kayar baya suka kwashe suka yi wa yankin kawanya.
"Birnin Timbuktu ya fuskanci hare-haren ta'addanci," a cewar sanarwar da rundunar ta fitar ranar Alhamis, inda ta yi kari da cewa an kashe mutane biyu tare da jikkata wasu mutum biyar.
Ko da yake a baya wasu majiyoyi biyu sun shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa mutane uku ne suka mutu.
''Masu tayar da kayar bayan sun yi harbi a Timbuktu, akalla fararen-hula uku ne suka mutu, cikinsu har da yara kanana," a cewar wani zababben jami'in gwamnati a Timbuktu a hira da AFP- adadin da majiyar wani asibiti ta tabbatar.
A watan Agusta wasu kungiyoyin ta'addanci masu alaka da Al Qaeda suka shelanta "yaki a yankin Timbuktu", sun gargadi masu manyan motocin da ke makwabtaka da su da kada su shiga birnin.
Bayan wata daya da rabi, dubban mazaunan yankin suka kusan katse alakarsu da duniya, sakamokon rashin walwala da shiga da fita daga yankin.
Kara Matsin lamba kan gwamnatin Mali
Shaidu sun bayyana wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa, suna rayuwa cikin fargaba da rashi, yayin da a bangare guda aka fara zuba musu ruwan harsashe, ga shi kuma uwa-uba suna karancin kayayyakin masarufi.
Mayakan dai na ci gaba da kai hare-hare a kauyukan da ke kusa da garuruwan da aka fi samun tsaro a arewacin Mali, alamu sun yi nuni da cewa suna kokarin kara matsi lamba ne kan gwamnatin tsakiya maimakon kwace garuruwan.
Gwamnatin mulkin soji na kasar Mali wacce ta karbe iko a shekarar 2020 na fuskantar kalubalen tsaro a duk fadin kasar amma ba ta wani mai da hankali ba ga halin da ake ciki a Timbuktu.