‘Yan sanda a Australiya sun tsinci kan alade a bakin kofar shiga wani masallaci

‘Yan sanda a Australiya sun tsinci kan alade a bakin kofar shiga wani masallaci

An sha samun al’amura masu alaka da kyamar Musulunci a birnin Graz na Australiya.
Da ‘yan sanda suka je wajen sai suka ga kan alade a daidai bakin kofar shiga masallacin. Hoto: OTHERS

An jefar da wani kan alade a bakin kofar shiga wani masallaci a birnin Graz na Australiya, kamar yadda wata kafar yada labarai ta ORF ta ruwaito a ranar Litinin 4 ga watan Satumba.

A cewar rahoton, wani mazaunin unguwar ne ya sanar da ‘yan sanda abin da ke faruwa da misalin karfe 9:40 na dare agogon kasar a ranar Lahadi.

Da ‘yan sanda suka je wajen sai suka ga kan alade a daidai bakin kofar shiga masallacin.

Ofishin da ke Kula da Kare Kundin Tsarin Mulki a yanzu ya karbi ragamar binciken.

Ba wannan ne karo na farko da irin hakan ke faruwa a birnin ba. An sha samun al’amura masu alaka da kyamar Musulunci a birnin Graz na Australiya.

A ranar 6 ga watan Mayun 2016, wani mutum ya makala kan alade a jikin kofar masallaci tare da yaryada jinin aladen a harabar masallacin.

Jim kadan bayan aikata hakan ne aka kama shi aka kuma yanke masa hukunci a 2020 tare da wasu mutum biyun da ke da hannu a lamarin.

A shekarar 2021, an sake gurfanar da wasu jami’an rundunar soji ta leken asiri da su ma aka same su da hannu a lamarin na 2016.

An zarge su da cewar sun san komai kan harin amma sai suka rufa wa wadancan asiri suka ki gaya wa ‘yan sanda lamarin.

Su ma an yanke musu hukuncin dauri da biyan tara tun a watan Janairun 2021, amma sun daukaka kara kuma ana ci gaba da sauraron karar.

TRT World