Kotun Ƙolin Venezuela ta ci kamfanin TikTok tarar dala miliyan 10 saboda "rashin aiwatar da matakan" kare yaduwar wani bidiyo na gasa da aka saka wanda ake zargin yaduwwarsa ta yi sanadiyar mutuwar yara uku 'yan Venezuela kwanan nan.
Mai Shari'a Tania D'Amelio ta fada a ranar Litinin cewa TikTok ya yi sakaci kuma ta bai wa kamfanin kwana takwas kacal don ya biya tarar, yayin da ta kuma umarce shi da ya bude ofis a Venezuela wanda zai kula da masu amfani da shi don tabbatar da bin dokokin kasar.
Alkaliyar ba ta bayyana ta yadda Venezuela za ta tilasta wa TikTok, wanda babban ofishinsa ke China ba tsarin biyan tarar.
Venezuela ta toshe shafukan intanet da dama a shekarun baya saboda rashin bin ka'idojin da hukumar sadarwarta ta gindaya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya tuntubi TikTok amma har zuwa yanzu kamfanin bai amsa ba.
A watan Nuwamba ne shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya zargi TikTok da alhakin mutuwar wata yarinya ‘yar shekara 12 da ake zargin ta mutu bayan ta shiga wata gasar bidiyo a TikTok da ya shafi shan kwayoyin kwantar da hankali da hana rashin barci.
Ministan Ilimi na Venezuela Hector Rodriguez shi ma ya fada a watan da ya gabata cewa wani matashi dan shekara 14 ya mutu bayan ya shiga wata gasar da aka yi a TikTok wanda ya hada da shan abubuwa.
Kuma a ranar 21 ga Nuwamba, babban lauyan Venezuela ya ɗora alhakin mutuwar wani yaron a kan TikTok bayan shiga gasar.