Umrah: Saudiyya ta bayyana dalilin soke bizar 'yan Nijeriya 264  bayan sun isa Jeddah

Umrah: Saudiyya ta bayyana dalilin soke bizar 'yan Nijeriya 264  bayan sun isa Jeddah

Gwamnatin Saudiyya ta ce 'yan Nijeriya da aka hana su shiga kasar domin yin aikin Umrah sun keta dokar mallakar biza.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin Nijeriya suka kulla wasu yarjejeniyoyin kasuwanci da Saudiyya, bayan ziyartar taron Kasuwanci na Saudiyya da kasashen Afirka da aka yi a birnin Riyadh./Hoto: Shafin Facebook na Bola Ahmed Tinubu

Gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewa ta soke bizar 'yan Nijeriya 264 da suka isa Jeddah daga jihohin Legas da Kano a ranar Lahadi ne saboda ba su cika ka'ida ba.

Ofishin jakadancin Saudiyya da ke Abuja ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba da maraice.

Batun hana ‘yan Nijeriya da suka isa Jeddah a jirgin Air Peace sauka a kasar Saudiyya ya jawo ce-ce-ku-ce musamman a shafukan intanet har ta kai ga gwamnatin Nijeriya ta sha alwashin gudanar da bincike.

Labari mai alaka: Nijeriya ta soma bincike a kan soke bizar 'yan kasar 264 da Saudiyya ta yi bayan isar su Jeddah

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin Nijeriya suka kulla wasu yarjejeniyoyin kasuwanci da Saudiyya, yayin taron Kasuwanci na Saudiyya da kasashen Afirka da aka yi a birnin Riyadh.

'Tsare-tsare da dokokin Saudiyya'

Sanarwar da ofishin jakadancin na Saudiyya ya fitar ta ce "fasinjojin da aka hana shiga" Saudiyya sannan aka "koma da su" kasarsu "ba su cika sharudan shiga Masarautar ba, saboda sun bayar da bayanan da ba daidai ba ne domin neman bizar da ba ita ya kamata su karba ba."

Sanarwar ta kara da cewa an gano hakan ne bayan sun isa Jeddah, abin da ya sa aka mayar da su Nijeriya.

"Ofishin jakadancin Masarauta yana jaddada wa masu zuwa ziyara muhimmancin bin tsare-tsare da dokokin Saudiyya. Kazalika, ya kamata dukkan fasinjoji su tantance takardunsu kafin su bar kasashensu zuwa Saudiyya. Wannan tsarin ba 'yan Nijeriya kadai ya shafa ba, har ma da dukkan kasashen duniya," in ji sanarwar.

TRT Afrika