Tsallake cin abinci: Masu samun kudi kadan a Jamus na shan wahala saboda tsadar gas

Tsallake cin abinci: Masu samun kudi kadan a Jamus na shan wahala saboda tsadar gas

Iyaye mata da ba su da aure da kuma iyalan da ba sa samun kudi da yawa na yawan bayyana a cibiyoyin bayar da tallafi --- wasu don samn kayan karatu da suke kokarin saya, wasu don samun na kaiwa bakunansu.

A ‘yan watannin da suka gabata ne Monique Ruck mai shekaru 34 dake da ‘ya’ya uku ta fara zuwa cibiyar walwala dake kusa da gidanta a gabashin babban birnin Jamus, cibiyar da wata kungiyar tallafawa yara matalauta ke kula da ita da ake kira Die Arche.

Mahaifiyar yaran su uku; masu shekaru 10, 7 da 2, ta fara zuwa cibiyar a cikin mako tare da wata kanwarta karama, suna hutawa, yin karatu sannan suna samun damar cin abincin rana tda kuniyar ke samarwa are da ‘ya’yan nata.

Mataki ne da ya zama dole Ruck ta dauka domin kula da kanta da yaranta, a lokacin da tsadar gas ke addabar Jamus, kasar ta Turai ta dogara ne kan Rasha don samun makamashi yayinda rikicin Yukren ya illata al’amarin.

A lokacin da take tattaunawa da TRT World, ‘yarta kuma tana wasa a wajen, ta ce iyalinta na cikin mawuyacin hali.

Ta ce “Ba farashin makamashi ne ya tashi ba, tsadar abinci da mota ma sun tashi sosai.”

Ta kara da cewa “Ina bukatar mota kullum don kai yara makaranta, amma ban san ya zan yi ba idan motar ta samu matsala ta tsaya. Na dam matuka game da watanni masu zuwa. Na san ba ni kadai ce a cikin irin wannan yanayi ba, kowa na shan wahala, amma akwai damwa saboda babu wanda ya san me zai je ya dawo.”

Kakakin Die Arch, Wolfgang Buescher ya shaida cewa kungiyar na taimakawa sama da iyalai dubu 5,000 da ba su da hali a fadin kasar, kuma akwai iyalai kamar 1,800 a Berlin --- kaso 95 din su kuma iyaye mata ne da ba su da maza – da suke bukatar tallafi a bangarorin shwarwari, abinci, shakatawa da ma ilimi. Ya fadawa TRT World cewa a shekaru 20 da suka gabata yana aiki a wannan gari, bai taba ganin yanayi mummuna kamar wannan ba.

Ya ce “Muna da iyaye da suke fada mana ba sa iya ciyar da yaransy da rana, a saboda haka suke tsallake abincin rana don su samu damar ba su abincin dare.”

Buescher ya kuma ce an samu raguwa daga samun tallafi daga wajen jama’a a ‘yan watannin nan, kuma suna sa ran adadin iyalan da za su tunkari kungiyarsu za su karu sosai.Ya kara da cewa “Akwai yiwuwar mu samu iyalai da dama daga Yukren da ma kasashen Larabawa wadanda suka zo a shekarun baya. Da wahala a yi hasashen mai zai faru a nan gaba.”

Abun ban mamaki matuka

Iyalai da mata kawai suke kula da su na daga cikin mafiya yawa dake fuskantar kalubale a lokacin da kasar ke fuskantar rikicin tattalin arziki da hauhawar farashi, wanda aka samu mafi yawa a cikin shekaru biyar da suka wuce.

Wani Injiniyar sarrafa bayanai haifaffiyar Indiya Abi Saripalli mai shekaru 34 tana rayuwa a Berlin kusan shekaru 10, kuma kwanan nan ta koma sabon gida dake kusa da tsakiyar birni. Matar mai aure da yarinya daya ita da mijinta sun riga sun fara neman mafita – shi ne su rage amfani da gas din su, saboda kamfanin dake ba su gas din ya gargade su.

Ta ce, “Muna biyan kusan Yuro 90 a wata a matsayin kudin gas da lantarki, amma an yi mana gargadi da cewa kudin zai iya ninkawa a wata.” Ta ci gaba da cewa “Kusan mun daina kunna na’urar dumama gida,kuma mn samo kayan sawa masu nauyi, tare da sauya kwayayen wutar lantarki da wadanda ba sa jan wuta sosai. Da safe akwai sanyi sosai, da yamma ma haka gari yake sanyi, dole mu saka rigunan sanyi. Daga Nuwamba, zai zama ana fuskantar sanyi mai tsanani, dole ne mu fara kunna abun sanyin da safe.”

Saripalli ta kuma ce ta lura da yadda wannan sauyi yake da sauki ga ‘yarta, sabanin ita da mijinta. Ta kara da “Ana wayar da kan yara sosai a makarantu game da yanayi, a saboda haka wannan ba sabon abu ne ga yara ba ko abun da zai ba su tsoro. Mu ba za mu zama kamar su ba saboda lokacin da muke yara ba a ba mu horon kare muhalli ba. Ni da mijina muna tunawa kawunanmu mu dinga kashe fitila ka sauran kayan lantarki. Ko idan na kunna ruwa yana zuba sosai, sai ta ce “Mommy ki kashe famfon saboda kifaye ba za su samu isasshen ruwa a kogi ba”.”

Kananan kasuwanci irin su gasa buredi, gidajen otel da masu samar da kayayyaki na fuskantar kalubalen. Kamfanunnukan Jamus 718 sun karye a watan Agusta, kari da kaso 26 sama da yadda yake a shekarar da ta gabata, kamar yadda Cibiyar Tattalin Arziki ta IH ta bayyana.

Wuraren motsa jiki da gyaran jiki, abubuwa ne sanannu a Jamus, na daga cikin bangarorin da suka sauya salon amfani da makamashinsu a lokacin da sanyi ke zuwa. Wani tsari ne da ya riga ya fara, in ji Helga Roehle mai shekaru 64 dake kula da wajen wanka na Hamam Berlin, wajen wankan Turkawa mafi tsufa a Jamus dake gundumar Kreuzberg ta kudu maso-gabas.

Tsohon kamfanin samar da kayan zaki dake a yanki mai manyan gine-gine, na Schokofabrik – ya kasance yana bayar da hidimar azuzuwa, wuraren motsa jiki da sauran aiyuka na mata da yara tsawon shekaru 40 - Hamam din ya dogara ne kan makamashi mai yawa da yake amfani da shi kwanaki bakwai na mako d ayake a bude.

Kamar yadda Roehle ta bayyana “Muna amfani da makamashi da yawa don dumama sauna da spa,kuma an fada mana farashin gas zai iya ninkawa har sau 6 sama da yadda muke biya a yanzu. Domin shiryawa lokacin sanyi dake tafe, mun fara daukar matakai kamar na samar da lantarki a sama rufin gininmu, sannan da rage yawan makamashin da ake amfani da shi a dakunan zafi.”

Roehle ta kara da cewa, wajen wankan na hamam dake da ma’aikatan safe da na dare, na da jimillar ma’aikata kusan 50, zai kara farashin aiyukansa, da suka hada da Kese (Gode dattin jiki) da Sabunlama (Tausa da sabulu) da kaso 10, wanda daga wannan watan sabon farashin zai fara aiki.

Ta ce “Yanayin da wajen wankan ke ciki shi ne abun damuwa. Ba m dade da fita daga kangin annoba ba d ata sanya aka rufe wajen, yanzu kuma tikicin Yukren, muna kallon illar sauyin yanayi. Muna fatan wannan abu zai kawo karshe nan ba da jimawa ba.”

TRT World