An naɗa Shoigu a matsayin ministan tsaron Rasha a 2012. / Hoto: Reuters Archive

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sauke ministan tsaron ƙasar Sergei Shoigu daga muƙaminsa a wani gagarumin garambawul da ya yi a fannin tsaron ƙasar a yayin da aka kwashe fiye da shekara biyu ana yaƙi da Ukraine.

Putin ya miƙa sunan masanin tattalin arziki Andrey Belousov ga majalisar dokokin ƙasar domin maye gurbin Shoigu, kamar yadda Majalisar Tarayyar ƙasar ta wallafa jerin sunayen sabbin ministocin ƙasar.

Putin ya sanar da cewa daga yanzu Shoigu zai zama sabon sakataren Majalisar Tsaron Rasha, inda zai maye gurbin daɗaɗɗen na hannun-damansa Nikolai Patrushev.

"Shoigu zai ci gaba da aiki a fannin tsaro, abin da yake da masaniya sosai a kai," kamar yadda kafar watsa labaran ƙasar ta ambato kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov yana bayyanawa.

"Ya san fannin ciki da waje, tare da abokan aikinsa da sauran masu ruwa da tsaki," in ji shi.

Kundin tsarin mulkin Rasha ya bai wa Putin damar miƙa sunayen sabbin mutane ko kuma waɗanda ke kan muƙamansu ga majalisar dokokin domin neman amincewar ta kafin ya naɗa su a muƙamai bayan zaɓen da ya lashe a watan Maris.

Ana sa rai 'yan majalisar dokokin Rasha za su amince da sabbin ministocin da Shugaba Putin ya miƙamusu ranar Talata.

An yi gagarumin garambawul a fannin tsaron ƙasar ne a yayin da dakarun Rasha suke ci gaba da mazayawa cikin fagen yaƙi a karon farko cikin watanni da dama.

An naɗa Shoigu a matsayin ministan tsaron Rasha a 2012.

Duk da koma-bayan da Rasha ta sha fuskanta a yaƙin Ukraine — waɗanda suka haɗa da gaza ƙwace babbar birnin ƙasar wato Kiev da janyewa daga birnin Kharkiv na arewa maso gabas da lardin Kherson na kudancin ƙasar — Putin bai sauke Shoigu daga kam muƙaminsa ba sai yanzu.

AFP