Gwamnatin Saudiyya a ranar Litinin ta yi gargaɗi dangane da tsananin zafi a Makkah a daidai lokacin da Musulmai ke shirin kammala Aikin Hajjin bana.
Wannan na zuwa ne bayan gomman mutane sun rasu sakamakon tsananin zafi a ‘yan kwanakin nan.
A sanarwar da gwamnatin ƙasar ta bayar, ta bayar da shawara ga mahajjata da su guji zuwa Jamrat, wato wurin Jifar Shaiɗan tun daga ƙarfe 11:00 na safe zuwa 4:00 na yama
An yi hasashen cewa a ranar Litinin, tsananin zafi a birnin Makkah zai iya kaiwa maki 49 a ma’unin Celsius, a daidai lokacin da mahajattan ke ci gaba da jifar sheɗan a Mina.
A ranar Lahadi kaɗai, an samu rahoton sama da mutum 2,700 da zafi ya yi wa illa, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta ƙasar ta tabbatar.
“Wurare masu tsarki a yau na fama da tsananin zafi mai girma tun bayan soma Aikin Hajjin bana... inda zai iya kaiwa maki 49 a ma’aunin Celsius, kuma muna nasiha ga mahajjata da kada su yawaita shiga rana,” kamar yadda ma’aikatar lafiyar ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar.
Ma'aikatar harkokin wajen Jordan a ranar Lahadin da ta gabata ta shaida cewa mahajjata 14 'yan kasar sun rasu "sakamakon zafin rana”.
Ita ma Iran ta ba da rahoton mutuwar mahajjata biyar, sai dai ba ta fayyace dalilin mutuwar tasu ba yayin da ma'aikatar harkokin wajen Senegal ta ce wasu uku su ma sun mutu.
Ma’aikatar Lafiya ta Saudiyya ta ƙara jaddada cewa mahajjatan sun tabbatar suna yawo da lema sannan su rinƙa shan ruwa sosai da kuma guje wa shiga rana.