Yawancinsu sun amince su sauya tufafin da ke jikinsu amma 67 sun ki yarda su cire abaya, kuma an kore su gida, a cewar ministan. / Hoto: AFP

Wani minista a Faransa ya ce an kori daliban da suka je makarantu sanye da abaya -- a ranar farko da aka koma makaranta bayan hutu.

Ministan Ilimi Gabriel Attal ya shaida wa gidan rediyon BFM cewa daliba kusan 300 ne suka bijire wa dokar haramta sanya abaya ranar Litinin.

Yawancinsu sun amince su sauya tufafin da ke jikinsu amma 67 sun ki yarda su cire abaya, kuma an kore su gida, a cewar ministan.

A watan jiya ne gwamnati ta sanar da haramta sanya abaya a makarantu, tana mai cewa Faransa kasa ce da babu ruwanta da addini.

Matakin ya faranta ran masu tsattsauran ra'ayi amma masu sasaucin ra'ayi sun ce hakan take hakkin mata Musulmai ne.

Labari mai alaka: Ba za mu janye dokar hana sanya abaya ba: Macron

Attal ya ce an bai wa daliban da suka ki cire abaya wasiku domin su kai wa iyayensu, ana mai shaida musu cewa matakin Faransa na "raba addini da lamuran hukuma, ba tarnaki ba ne".

Idan suka sake komawa makaranta sanye da abaya za a yi "sabuwar tattaunawa", a cewar ministan.

Ranar Litinin da maraice, Shugaba Emmanuel Macron ya kare wannan mataki wanda ya jawo ce-ce-ku-ce, yana mai cewa akwai wasu "tsirarun" mutane a Faransa da suka yi "garkuwa da addini kuma suna kalubalantar tsarin jamhuriya da matsayin Faransa na raba addini da lamura na hukuma."

Ya kara da cewa irin wannan ra'ayi ne ya sa kashe wani malami mai suna Samuel Paty saboda ya yi zanen batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a yayin da yake yin darasi a aji.

"Ba za mu yi shiru kamar ba a kai hari da ya kashe Samuel Paty ba," in ji Macron a wata hira da aka yi da shi a shafin You Tube na HugoDecrypte.

Wata kungiyar Musulmai ta gurfanar da gwamnatin Faransa a kotu kan haramta sanya abaya.

Za a soma shari'a kan karar da kungiyar ta Action for the Rights of Muslims (ADM) motion ta shigar ranar Talata.

Wata doka da aka kaddamar a Faransa a 2004 ta "haramta wa dalibai sanya duk wata alama da ke nuna wani addini " a makarantu.

AFP