Joan E Donoghue, shugabar kotun kasa da kasa, ta karanta hukuncin da ake ta jira wand alkalai 17 suka yanke. / Hoto: Reuters  

Kotun hukunta manyan laifuka ta Majalisar Dinkin Duniya ICJ ta umarci Isra'ila da ta dauki dukkan matakan da za ta iya dauka wajen dakile aikata kisan kiyashi a Gaza.

A umarnin da kotun ta bayar a ranar Juma'a a ta kuma umarci Isra'ila da ta saukaka ayyukan jinkai a yankin da aka yi wa kawanya.

Kotun ICJ ta ce tana da hurumin yanke hukunci kan matakan gaggawa, tana mai cewa ba za ta yi watsi da batun kisan kare-dangi ba kamar yadda Isra'ila ta bukata.

Kazalika ta bayyana Falasdinawa a matsayin wata al'umma da ke da kariya a karkashin yarjejeniyar kisan kare-dangi, tana mai jaddada cewa ta amince da hakkin Falasdinawa a Gaza na samun kariya daga ayyukan kisan kare-dangi.

A ranar 29 ga watan Disamba ne kasar Afirka ta Kudu ta shigar da kara a gaban kotun ICJ inda ta bukaci a hukunta Isra'ila saboda harin da take kaiwa Gaza ya sabawa yarjejeniyar kisan kare-dangi..

Daga cikin bukatun matakan da Afirka ta Kudu ta nema, akwai bukatar gaggawa na dakatar da Isra'ila daga kai mumunarn hare-hare wanda ta sanadiyar kashe Falasdinawa sama da 26,000, a cewar hukumomin lafiya na Gaza.

Haka kuma kasar ta bukaci kotun ICJ ta ba da umarni a hukumance saboda gaggawar lamarin.

Bayan kammala sauraren karar a ranakun 11 zuwa 12 ga watan Janairu, kotun ta fara tattaunawa bayan ta yi nazari kan abubuwan da bangarorin suka gabatar da kuma shaidu.

TRT World