Kimanin Musulmai miliyan biyu ne ake sa rai za su gudanar da aikin hajjin bana. / Hoto: AA

A ranar Juma'a ne Alhazai suka fara aikin Hajji na shekarar 2024, inda suka fita birnin Mina, wanda ake yi wa laƙabi Birnin Tantuna.

Ana sa ran alhazan za su shafe tsawon yinin ranar Juma'ar takwas ga watan Zul-Hajji su kuma wayi gari a birnin na Mina, sannan su fita Filin Arafat ranar Asabar 9 ga watan na Babbar Sallah.

Ana kiran ranar fita zuwa Mina da Ranar Tarwiyya a harshen Larabci, saboda tun a zamanin da alhazai sukan yi tanadin ruwan da za su tafi da shi Mina daga Makka, saboda a lokacin babu ruwan sha a Mina ɗin.

Wani Alhaji daga Nijeriya Rabi'u Biyora ya shaida wa TRT Afrika cewa "wajen ƙarfe takwas na daren jiya alhazan Legas suka fita Mina, sannan su ma alhazan jihar Jigawa sun fita wajen ƙarfe ɗayan dare."

Ya ƙara da cewa, amma har zuwa safiyar yau Juma'a ana ci gaba da fita, "Mu ma sai nan gaba za mu ƙarasa," a cewar Biyora.

Wasu alhazan Nijeriya yayin da suke shirin tafiya Mina don fara aikin Hajjin 2024. / Hoto: Rabiu Biyora

Aikin Hajji na ɗaya daga shika-shikan Musulunci biyar, wanda ya wajaba a kan dukkan Musulmi mai hali, aƙalla sau ɗaya a rayuwarsa.

Tun a daren Juma'a ne dubban mahajjata suka fara fita zuwa Mina, a wani mataki da hukumomi suke ɗauka na rage cunkoso, sannan sauran alhazan za su isa Mina a ranar Juma'a.

Dukkan alhazai na kasancewa cikin harami lokacin fita Mina, inda maza ke ɗaura zani da mayafi farare, sannan mata kuma suke sanya ko wane irin nau'in tufafi da ya dace da ibadar.

Tun a daren Juma'a wasTun a daren Juma'a wasu alhazan suka fara fita Mina domin fara aikin Hajjin na 2024. / Hoto: Haramain

Fita Mina ranar takwas ga wata na daga cikin muhimman abubuwan da ake yi a lokacin aikin Hajji, "to sai dai ba ta daga cikin rukunan na aikin na Hajji," a cewar Farfesa Mansur Isa Yelwa, wani malamin addinin Musulunci a Nijeriya, wanda kuma yake halartar aikin Hajjin na bana.

Farfesa Mansur Yelwa ya ce manyan rukunan aikin na hajji guda huɗu ne, da suka haɗa da Niyya, da Tsayuwar Arfa da Ɗawaful Ifada da kuma Sa'ayi (tsakanin Safa da Marwa).

"To amma akwai wasu muhimman ibadu da Musulunci ya shar'anta su yayin aikin na Hajji, da suka haɗa da kwana a Muzdalifa, da yin jifa, da yanka dabbar hadaya da aski, da kuma zaman kwanaki biyu ko uku a Mina," a cewar Farfesa Mansur Yelwa.

Bayan Alhazai sun shafe yinin Juma'a sun kuma wayi garin Asabar, za su tafi filin Arfa, inda za su shafe yinin ranar a can. Tsayuwar Arfa ita ce Ibada mafi girma a aikin hajji, kamar yadda Farfesa Mansur Yelwa ya bayyana wa TRT Afrika Hausa.

Hukumomin Saudiyya sun ce fiye da mutum miliyan 1.5 ne suka isa ƙasar zuwa tsakiyar makon nan don ibadar ta Hajjin bana. Ana sa ran kimanin mutum miliyan biyu ne za su yi aikin Hajjin na bana.

Malamin na addinin Musulunci ya ƙara da cewa akwai kuma wasu abubuwa da dole ne mai aikin Hajji ya kiyaye aikata su lokacin da ake tsaka da ibadar, idan har yana so ibadar tasa ta zama karɓabbiya.

Ya ce sun haɗa da yake farce da aski da ƙaurace wa iyali, da rashin sanya turare, "don mutum ya nuna ƙanƙan da kai, kuma ba komai ba ne a wajen Allah," in ji Farfesa Yelwa.

Tsananin zafin rana

Aikin Hajjin na bana na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar tsananin zafin rana a wasu ƙasashen duniya, ciki har da Saudiyya.

Hukumomi sun yi gargaɗin cewa za a fuskanci tsananin zafi lokacin aikin Hajjin na bana. Zafin zai kai maki 40 na zafi a ma'aunin salshiyos a ranar Juma'a, sannan a ranar Asabar, ranar Arfa kuma ana hasashen zai iya kaiwa maki 45.

Ma'aikatar Lafiya ta Saudiyya ta yi gargaɗin cewa tsananin zafi "zai kasance cikin manyan ƙalubalen da mahajjata za su fuskanta a bana," kamar yadda kafofin watsa labaran Saudiyya suka rawaito ranar Talata.

Ma'aikatar ta shawarci mahajjata da suka ƙaucewa shiga rana ba tare da wata kariya ba, sannan su yawaita shan ruwa, su rage cunkusuwa waje guda, sannan a ringa cin abubuwa masu ruwa-ruwa irin su kayan marmari, kamar yadda kafofin watsa labaran Saudiyya suka ruwaito.

TRT Afrika da abokan hulda