Wasu Falasdinawa na duba baraguzan masallacin Yassin da aka lalata bayan wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai a sansanin 'yan gudun hijira na Shati da ke Gaza. / Hoto: AP         

Kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza tare da mamaye mashigar Rafah da ke kan iyakar Gaza da Masar, sun hana Falasɗinawa 2,500 tafiya Saudiyya don gudanar da aikin Hajjin bana, kamar yadda Ma'aikatar Addini ta sanar.

A fili ƙarara ''hakan ya bayyana cin zarafi da take hakkin masu gudanar da addini,'' kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar Ikrami Al- Mudallah ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Anadolu a ranar Alhamis.

Yaƙin ya hana ma'aikatar kammala shirye-shiryen aikin Hajji da aka saba yi, cikin har da sanya hannu kan kwangilolin sufuri a Masar da Saudiyya da kuma ba da masauki a biranen Makkah da Madina, in ji shi.

Al-Mudallal ya bayyana cewa "rufe mashigar Rafah da yaƙin da ake yi sun hana alhazan Gaza 2,500 ciki har da tawagar da za su yi rakiya zuwa aikin Hajjin na bana.''

“Tawagar tana wakiltar kashi 38 cikin 100 na alhazan Falasɗinawa 6,600,” in ji shi.

Al-Mudallal ya ce ma'aikatar tana tuntuɓar hukumomin da abin ya shafa a Saudiyya da Masar domin shawo kan matsalar da ta bayyana a matsayin ''tauye hakkin'' alhazan Falasɗinu tare da neman hanyoyin da za a iya bi don ganin sun samu damar zuwa aikin Hajji.

Ya ba da tabbacin cewa maniyyatan da abin ya shafa a bana “ba za su rasa ‘yancinsu na zuwa aikin Hajji a shekara mai zuwa ba", yana mai ba da tabbacin cewa za a fi ba da fifiko a kansu a gaba musamman ganin da yawa sun jira tsawon shekaru kafin lokaci ya kawo kansu kuma kashi 70 cikin ɗari tsofaffi ne ko kuma marasa lafiya.

Karamcin Masauratar Saudiyya

A wannan shekara, Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz ya ba da damar karɓar baƙuncin mahajjata 500 daga 'yan'uwan waɗanda suka jikkata ko aka kashe a Gaza da ke wajen yankin da aka mamaye, a cewar Al-Mudallal.

“Wannan karamcin ya bai wa waɗanda suka baro Gaza damar gudanar da aikin Hajji, yanayin da bai wa Gaza damar cin moriyar karamcin Masauratar Saudiyya,'' in ji shi.

A ranar 6 ga watan Yuni ne Sarkin Saudiyya ya ba da umarnin karɓar baƙuncin mahajjata 1,000 daga iyalan waɗanda aka kashe ko aka jikkata a Gaza a wani ɓangare na shirin Hajji da Umrah na ma'aikatar harkokin addinin Musulunci ta Saudiyya.

An zaɓi mahajjatan ne daga cikin waɗanda suka baro Gaza ko dai saboda yaƙi ko kuma don neman magani.

A watan Maris na shekarar 2023 ne Ma'aikatar Addini ta Gaza ta gudanar wani tsari na canki-canki don zaɓar mahajjatan da za su yi aikin Hajji a 2023 da kuma 2024 saboda ƙarancin gurbi da kuma mamayen Isra'ila, tana mai ba da fifiko kan tsofaffi da marasa lafiya.

Ma'aikatar ta yi Allah wadai da lamarin a ƙarshen watan Mayu, tana mai cewa ta'addancin da Isra'ila ke ci gaba da yi da kuma mamayar mashigar Rafah da kuma hare-hare tun daga ranar 7 ga watan Mayu sun hana a kammala shirye-shiryen tafiya aikin Hajjin bana ga alhazan Gaza.

Kazalika ma'aikatan ta kira hakan da "keta 'yancin addini da dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa."

Kisan ƙare-dangi

Isra'ila ta kashe aƙalla Falasɗinawa 37,202 - kashi 70 cikin 100 mata ne da yara da kuma jarirai- tare da jikkata mutum 84,932 da kuma binne fiye da mutum 10,000 da ransu a ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka kai musu hari.

Hukumomin Isra'ila ne suke da alhakin "laifukan yaƙi da cin zarafin bil'adama da aka aikata" a lokacin hare-haren da suka kai Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, a cewar wani kwamitin gudanar da bincike da Majalisar Ɗinkin Duniya ke marawa baya.

Kwamitin binciken, wanda kwamitin kare hakkin bil'adama na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kafa, ya bayyana cewa "an yi ta kai hare-hare masu yawa kan fararen-hula a Gaza" ciki har da "hari na yunwa a matsayin wata dabara ta yaƙi".

Falasɗinawa na ci gaba da fuskantar matsalar yunwa saboda Isra'ila ta katse hanyoyin abinci da magunguna da sauran kayayyaki da ke shigo yankin.

Hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce sama da mutane miliyan 1 daga cikin mutane miliyan 2.4 a Gaza za su iya fuskantar matsalar yunwa a tsakiyar watan Yuli.

Sannan a Kotun ƙasa da ƙasa ma, ana tuhumar Isra'ila da aikata kisan kiyashi kan Falasɗinawa.

TRT World