Musulmai sun taru a Dutsen Arafat don gudanar da wannan ibada da ta kasance wajibi ga dukkan mahajjaci ranar 15 ga watan Yuni, 2024. / Hoto: AP

Musulmai daga faɗin duniya sun taru a Dutsen Arafat da ke kudu maso gabashin birnin Makkah inda za su wuni suna gudanar da ibada a cikin rana, don sauke wannan farali kamar yadda yake a rukunan Aikin Hajji.

Ana kallon Hawan Arafat, wanda ake yi wa laƙabi da dutsen rahama, a matsayin ƙololuwar Aikin Hajji. Yana cikin ibadun da mahajjata suka fi tunawa da su, inda suke tsayawa kafaɗa da kafaɗa, suna addu'o'in neman gafara daga wurin Allah mai girma. Dutsen yana da nisan kilomita 20 daga kudu maso gabashin Makkah.

Hadisai sun nuna cewa Annabi Muhammah (SAW) ya gabatar da Huɗubar Bankwana a Dutsen Arafat shekaru 1,435 da suka gabata. A cikin huɗubar, manzon Allah ya yi kira game da daidaito da haɗin-kai tsakanin Musulmai.

"Wannan yanayi ne da ba zai misaltu ba," a cewar Ahmed Tukeyia, wani mahajjaci ɗan ƙasar Masar, a yayin da ya isa tantinsu da ke Dutsen Arafat ranar Juma'a da maraice.

Hajji shi ne taron addini mafir girma a duniya. An soma gudanar da Aikin Hajjin bana ne ranar Juma'a yayin da Musulmai suka tafi daga Masallacin Harami zuwa Mina da ke wajen birnin Makkah.

Hukumomin Saudiyya sun ce suna sa rai mahajjatan bana su zarta mutum miliyan biyu.

Aikin Hajji yana cikin shika-shikan Musulunci guda biyar. Wajibi ne kowane Musulmi da ke da hali - lafiya da kuɗi - ya gudanar da aikin Hajji aƙalla sau ɗaya a rayuwarsa.

TRT World