1625 GMT — Kotun ICJ ta umarci Isra'ila da ta dauki matakan magance yunwar da ake fama da ita a Gaza
Alkalai a kotun kasa da kasa baki dayansu sun bai wa Isra'ila umarnin daukar dukkanin matakan da suka dace kuma masu inganci don tabbatar da isar kayayyakin abinci na yau da kullun ga al'ummar Falasdinu a Gaza.
Kotun ta ICJ ta ce Falasdinawa a Gaza na fuskantar mummunan yanayi na rayuwa kuma yunwa da tsananin rashin abinci na yaduwa.
"Kotu ta lura cewa Falasdinawa a Gaza ba barazanar yunwa kawai suke fuskanta ba (...) mummunan fari ma ya kunno kai," in ji alkalan a cikin umarninsu.
Kasar Afirka ta Kudu ce ta bukaci sabbin matakan a matsayin wani bangare na shari’ar da take ci gaba da yi na zargin Isra’ila da kisan kiyashin da take yi a Gaza.
0950 GMT — Sojojin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa fiye da 200 a asibitin Gaza
Sojojin Isra'ila sun kashe fiye da Falasɗinawa 200 a wani samame da ta kai Asibitin al-Shifa dake birnin Gaza, a cewar rundunar sojin.
Wata sanarwar rundunar sojin ta ce har yanzu dakarun suna cikin asibitin suna fafatawa.
Ta ƙara da cewa, "An kawar da masu zagon ƙasa kusan 200."
Rundunar ta yi ikirarin cewa dakarunta sun kwashe fararen hula da marasa lafiya, da ma'aikatan lafiya zuwa wani bangare na asibitin "wanda sojojin suka shirya kuma suka kafa don ba da damar ci gaba da kula da lafiya."
Sojojin Isra'ila sun kai farmaki kan asibitin da cibiyar kiwon lafiya mafi girma a Gaza da ke dauke da dubban marasa lafiya da kuma mutanen da suka rasa matsugunansu, a ranar 18 ga Maris.
0250 GMT — Isra'ila za ta sayi tantuna 40,000 daga China a shirinta na kai farmaki Rafah
Kamfanin dillancin labaran Isra'ila ya rawaito cewa Firaminista Benyamin Netanyahu ya bayar da umarnin sayen tantuna 40,000 daga kasar China da za a kafa a Zirin Gaza da aka yi wa ƙawanya, a shirye-shiryen kai farmaki ta kasa a Rafah inda Falasdinawa sama da miliyan 1.5 da suka rasa matsugunansu ke samun mafaka.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Netanyahu ya yi watsi da fargabar da duniya ke da shi na fuskantar bala'in jinƙai idan Isra'ila ta kai farmaki ta kasa a yankin kudancin Gaza, yana mai cewa fararen hula za su iya tserewa fadan zuwa wasu sassan yankin da yaƙi ya ɗaiɗaita.
Da yake magana da tawagar majalisar dokokin Amurka da ke ziyara a Isra'ila, Netanyahu ya ce mutanen da ke mafaka a Rafah - fiye da rabin al'ummar Gaza miliyan 2.3 - za su iya ficewa daga faɗan.
"Kawai mutane su tafi, su tafi da tantunansu," in ji Netanyahu a cikin kalamansa na izgilanci. "Mutane sun koma Rafah. Suna iya sake barin can ɗin ma."
Kutsen da Isra'ila ke shirin yi ya tayar da hankulan duniya saboda birnin, wanda ke kan iyakar Gaza da Masar yana cunkushe da Falasdinawa sama da miliyan 1.5 a sansanoni da tantuna da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa, wadanda galibinsu suka tsere daga hare-haren da Isra'ila ke kaiwa wasu wurare.
0142 GMT — Kungiyar Musulman Amurka ta yi kira da a gudanar da bincike a Majalisar Dinkin Duniya kan bidiyon da sojojin Isra'ila ke harbewa tare da binne Falasdinawa
Majalisar da ke kula da dangantakar Amurka da Musulunci (CAIR) ta yi kira da a gudanar da bincike na Majalisar Dinkin Duniya kan wani bidiyo da ke nuna sojojin Isra'ila suna harbe wasu Falasdinawa biyu tare da binne su da wata katafila.
"Wannan danyen aikin na yaki da sauran laifuka da makamantansu da gwamnatin Isra'ila mai kisan kiyashi ke aikatawa a kullum, dole ne MDD ta yi bincike a kai a wani bangare na ci gaba da aiwatar da kisan kare dangi da kawar da wata al'umma da azabar yunwa da ake gana wa al'ummar Falasdinu tare da hadin gwiwar gwamnatin Biden," in ji Daraktan Sadarwa na CAIR Ibrahim Hooper a wata sanarwa da ya fitar.
Ya ƙara da cewa "Dakarun gwamnatin Isra'ila masu tsattsauran ra'ayi da alama suna kashe Falasdinawa ne da son rai, sannan kuma suna daukar gawarwakinsu tamkar bola, dole ne a dakatar da wannan kisan kiyashi, ba wai ba da uzuri ko tallafa musu da makamai da maganganu ba."