Gallant ya kuma ce ya tattauna da manyan jami'an Amurka "kwana daya bayan" shawarwarin da ya gabatar na gudanar da mulki bayan kammala yaƙin Gaza, / Photo: Reuters

1308 GMT –– A shirye muke mu yaƙi Hezbollah idan har ta kama: Ministan Tsaron Isra'ila

Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce sojojin Isra'ila za su kasance a shirye don daukar duk wani matakin da ya dace kan kungiyar Hezbullah ta kasar Labanon, ko da yake abin da ake so shi ne cimma matsaya ta shawarwari.

Muna kai wa kungiyar Hezbollah hari sosai a kowace rana kuma za mu kai ga cikakken shiri na daukar duk wani mataki da ake bukata a kasar Labanon, ko kuma cimma wani shiri daga matsayi mai ƙarfi. Mun fi son tsari, amma idan aka kai mu maƙura za mu san yadda za mu yi yaƙi,” an ruwaito Gallant a wata sanarwa da ofishinsa ya fitar.

1236 GMT Aƙalla Falasɗinawa bakwai aka kashe sannan aka jikkata 17 a lokacin da jirgin yaƙin Isra’ila maras matuƙi ya jefa bam kan taron wasu farar hula a lokacin da ke shirin komawa unguwar Shujaiya da ke gabashin Gaza, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA ya bayyana.

Falasɗinawa uku suka rasu a lokacin da jirgin ya jefa musu bam a cikin motar da suke ciki a sansanin gudun hijira na Maghazi da ke tsakiyar Gaza.

An aika da mutanen uku waɗanda suka rasu a asibitin Alqsa wanda ke a unguwar Deir Al Balah.

2240 GMT — Babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce yunƙurin hanzartawa da daidaita aikin kai kayan agaji zuwa faɗin Falasɗinu ya samu "tasgaron ƙalubale", kuma kai kayayyakin ya yi "ƙasa sosai" tun da Isra'ila ta ƙaddamar da harin soji a kudancin birnin Rafah ranar 6 ga Mayu.

Sama da al'ummar Gaza miliyan 1.9 daga cikin miliyan 2.3 sun tagayyara, kamar yadda Sigrid Kaag ta faɗa wa Kwamitin Tsaro na MDD.

Ta ce harkar lafiya ta ruguje, an rusa makarantu, kuma zafin yanayi yana ƙaruwa, ga kuma ƙarancin ruwan sha da tsaftar muhalli, “haɗarin ɓarkewar cututtuka masu yaɗuwa yana ƙaruwa.”

“Babu wani zaɓi ban da na aniyar siyasa, da cikakken girmama dokokin kare ɗan-adam, musamman kare farar hula, da samar da kyakkyawan yanayi don rarraba kayan agaji,” cewar Kaag, babbar jami'ar MDD kan agaji da sake gina Gaza.

0330 GMT — Isra'ila ta kashe gomman Falasɗinawa a hare-haren da ta kai Zirin Gaza

Isra’ila ta kai wasu sabbin jeri hare-hare a Birnin Gaza, inda ta kashe gomman Falasɗinawa fararen hula, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasɗinawa WAFA ya bayyana, inda yace an samu rahotannin jikkata mutane daga yankunan Sheikh Radwan da Shujaeya da kuma gabashin Birnin Gaza.

Tun da farko, Isra’il ta kashe aƙalla fararen hula 12, ta kuma jikkata wasu a hare-haren jiragen sama a Deir al Balah a tsakiyar Gaza da aka mamaye, kamar yadda WAFA ya rawaito.

Wakilin WAFA ya ce an kai gawawwakin mutane 12 Asibitin Shahidai na Al-Aqsa a Deir al Balah bayan hare-haren sama kan gidan iyalen Eslayyim a birnin.

Isra’ila ta kuma kashen wasu fararen hular uku a yankin Al-Mansura a unguwar Shejaiya, da wasu ukun kuma daban a yammacin Rafah, a cewar kamfanin dillnacin labaran.

Hukumomin lafiya sun shaida wa WAFA cewa daga wayewar gari an kai aƙalla gawawwakin fararen hula 31 asibitocin yankin.

TRT World