Isra'ila tana tuhumar limamin Masallacin Ƙudus da kalaman tunzura ta'addanci. / Hoto: AA / Photo: AA Archive

1221 GMT — Isra'ila tana tuhumar limamin Masallacin Ƙudus da kalaman tunzura ta'addanci

Limamin Masallacin Ƙudus ya yi Allah-wadai da wani kamfen na "ƙarya" da aka ƙirƙira da nufin adawa da shi bayan da aka tuhume shi da laifin ta da kayar baya bisa zargin yabon Falasdinawa 'yan bindiga da suka kashe 'yan Isra'ila hudu ciki har da soja daya.

Sheikh Ekrima Sabri, mai shekaru 85, tsohon mufti ne na Birnin Kudus, kuma a yanzu shi ne shugaban Majalisar Ƙoli ta addinin Musulunci a Birnin Kudus, yana wa'azi a wurin da aka mamaye a Gabashin Kudus mai tsarki.

Sheikh Ekrima Sabri, mai shekaru 85, tsohon muftin Birnin Kudus, kuma a yanzu shi ne shugaban majalisar koli ta addinin musulunci a birnin Kudus, yana wa'azi ne a wurin da aka mamaye a gabashin Kudus mai tsarki.

An tuhumi Sabri a wannan makon da laifin tunzura ta’addanci saboda kalaman da ya yi wadanda ake zargi na goyon bayan wani maharin da ya harbe masu gadi a matsugunin Yammacin Kogin Jordan da ke Maale Adumim, inda ya kashe wani soja a watan Oktoban 2022.

1137 GMT —Adadin Falasɗinawa da Isra'ila ta kashe a yaƙin Gaza ya kai 37,765

Adadin Falasɗinawa da Isra'ila ta kashe a yaƙin da take yi a Gaza ya kai 37,765 bayan ta kashe ƙarin Falasɗinawa 47, a cewar Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta yankin.

Kazalika Isra'ila ta jikkata Falasɗinawa aƙalla 86,429 tun da ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza ranar 7 ga watan Oktoban 2023, in ji ma'aikatar.

"Dakarun Isra'ila ta kashe ƙarin Falasɗinawa 47 sannan ta jikkata 52 a hare-haren ƙare-dangi da ta kai a gidajensu a awanni 24 da suka gabata," kamar yadda ma'aikatar ta ƙara da cewa.

1001 GMT —MDD ta soki Isra'ila saboda amfani da karkuna don musguna wa Falasɗinawa fursunoni

Mai magana da yawun Hukumar Kare Hakkin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya (OHCHR) Jeremy Laurence ya soki sojojin Isra'ila kan amfani da karnuka wajen musguna wa Falasɗinawa fursunoni.

Laurence ya bayyana haka ne a amsar tambayoyin da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya tura masa game da sojojin da suke amfani da karnuka domin musguna wa Falasɗinawa fursunoni, da yin lalata da su da kuma yin amfani da Falasɗinawa da suka jikkata a matsayin garkuwar yaƙi a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye.

“Mun samu rahotanni da ke nuna cewa an yi amfani da karnuna wajen musguna wa tsararru, a wasu lokutan suna kai musu hari da cizonsu,” in ji Laurence.

“Hakan babban keta hakki ne na mutanen kuma ya saɓa wa dokokin kare hakkin ɗan'adam da suka jiɓanci damar da mutum yake da ita ta gudanar da rayuwa da samun kiwon lafiya,” a cewar Laurence.

Jeremy Laurence ya soki sojojin Isra'ila kan amfani da karnuka wajen musguna wa Falasɗinawa fursunoni. / Hoto: Reuters

0759 GMT —Dakarun Isra'ila sun kai samame a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin a gaɓar Yammacin Kogin Jordan

Sojojin Isra'ila sun kai samame a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin da ke gaɓar Yammacin Kogin Jordan a yayin da suke ci gaba da fafatawa da mazauna yankin, a cewar ganau.

Dakarun na Isra'ila sun lalata gidaje da kantuna da dama a yayin samamen sannan suka kama Falasɗinawa takwas kafin su fice daga sansanin, in ji mazauna wurin.

Ƙungiyar Bayar da Agaji ta Palestinian Red Crescent Society ta ce likitocinta sun kula da Falasɗinawan da suka jikkata sakamakon harbin bindiga a Jenin.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce an kashe wani sojanta yayin da aka jikkata mutum 16 a yayin samamen.

Dakarun na Isra'ila sun lalata gidaje da kantuna da dama a yayin samamen sannan suka kama Falasɗinawa takwas kafin su fice daga sansanin, in ji mazauna wurin. / Hoto: AA

0130 GMT —A shirye MDD take ta tura 'yan sanda zuwa Gaza, in ji wani jami'i

A shirye Majalisar Dinkin Duniya take “ta amince da bukatar duk wata kasa" mambarta ta tura 'yan sanda zuwa Gaza, in ji Mataimakin Sakatare Janar na MDD kan sha'anin Wanzar da Tsaro.

"Idan wata hukuma ta kira mu taimaka, tabbas za mu yi bakin kkarinmu," a cewar Jean-Pierre Lacroix, yayin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida a hedkwatar MDD da ke New York.

Da yake bayani kan batutuwa da dama game da rarraba tallafi a Gaza, Lacroix ya ce ana samun karuwar satar kayan abinci a yankin.

Ya jaddada bukatar samun mafita daga wadannan matsaloli, yana mai cewa akwai yiwuwar su yi amfani da wasu hanyoyi don cim ma muradunsu.

An kai wasu yara Falasdinawa asibiti bayan Isra'ila ta yi luguden wuta a wani gida da ke Beit Lahia, Gaza. / Hoto: AA

0023 GMT — Ministan Tsaron Isra'ila Gallant ya yi barazanar mayar da Lebanon zuwa "Zamanin Dutse"

Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant a wata ziyara da ya kai birnin Washington ya bayyana cewa sojojin Isra'ila suna da ikon mayar da kasar Lebanon "komawa zamanin dutse" a duk wani yaƙi da za ta yi da kungiyar Hizbullah, amma ya dage cewa gwamnatinsa ta fi son a samar da hanyar diflomasiyya a kan iyakar Isra'ila da Lebanon.

Da yake zantawa da manema labarai, Gallant ya kuma ce ya tattauna da manyan jami'an Amurka "kwana daya bayan" shawarwarin da ya gabatar na gudanar da mulki bayan kammala yaƙin Gaza, wanda zai hada da Falasdinawa na gida da abokan hulɗa na yanki da kuma Amurka, amma hakan zai kasance "tsari mai tsawo da sarƙaƙiya. "

Gallant ya kuma ce ya tattauna da manyan jami'an Amurka "kwana daya bayan" shawarwarin da ya gabatar na gudanar da mulki bayan kammala yaƙin Gaza, / Photo: Reuters

2200 GMT — Isra’ila ta kashe mutum biyu a Syria, ta raunata biyar a Lebanon

Isra'ila ta kashe mutane biyu tare da raunata wani soja daya bayan da ta kai hari a kudancin Syria, kamar yadda kafafen yada labaran gwamnatin Syria suka rawaito.

Kamfanin dillancin labaran gwamnatin ƙasar, SANA ya rawaito cewa an kai hare-hare a wurare da dama a kudancin Syria, lamarin da ya haifar da ɓarna a yankin Tuddan Golan da Isra’ila ta mamaye, ba tare da bayar da karin bayani kan inda aka kai hare-hare da ɓarnar da aka yi ba.

A kasar Labanon, Isra'ila ta raunata mutane biyar bayan ta kai hari kan wani bene mai hawa biyu a garin Nabatiyeh da ke kudancin kasar Lebanon, kamar yadda kafar yada labaran kasar ta rawaito.

2200 GMT — Majalisar Dinkin Duniya ta kasa amfani da hanyar da Isra'ila ta amince a bi wajen isar da agaji

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba ta iya yin amfani da hanya daya tilo da Isra'ila ta amince da ita ta kai kayan agaji zuwa kudancin Gaza da aka yi wa ƙawanya saboda karuwar aikata laifuka da kuma kisan kiyashi da Isra'ila ke yi a kusa da wajen.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric ya shaida wa manema labarai cewa, hukumomin Isra'ila na ci gaba da takaita amfani da wasu hanyoyi zuwa hanyar da aka keɓe daga Karem Abu Salem - hanya daya tilo da ke tsallakawa daga Isra'ila zuwa kudancin Gaza - zuwa babbar hanyar Salah a-Din, babbar hanyar arewa da kudu.

"Hanyar da aka ce mu yi amfani da ita wajen shiga Kerem Shalom yanzu ba ta da tsaro a gare mu saboda karuwar aikata laifuka, don haka ba mu samu damar yin amfani da wannan hanyar ba."

TRT Afrika da abokan hulda