Yahudawan, waɗanda suka samu kariya daga wurin dakarun Isra'ila, sun riƙa yin abubuwan da za su tunzura mutanen da ke cikin masallacin yayin da suka gudanar da ibadun Talmud.  / Hoto: AA

1310 GMT — Isra'ila za ta ci gaba da yaƙi a Gaza har zuwa farkon 2025 — Tel Aviv

Babban mai bai wa Firaminista Benjamin Netanyahu shawara kan tsaro ya ce Isra'ila ba za ta gama yaƙin da take yi a Gaza ba har sai farkon shekarar 2025.

Tzachi Hanegbi ya shaida wa kafar watsa labaran gwamnatin ƙasar cewa ana sa ran za a ci gaba da yaƙin har nan da wasu watannin bakwai.

Isra'ila tana ta faɗaɗa hare-harenta a Rafah a ranar Talata, inda tankokin yaƙinta suka isa tsakiyar birnin.

0901 GMT Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna sun mamaye Masallacin Ƙudus don yin ibadun Talmudi

Gomman Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna sun mamaye Masallacin Ƙudus da ke Gabashin Birnin Ƙudus a yayin da aka taƙaita wa Falasɗinawa shiga Masallacin.

Kamfanin dillancin labaran Wafa na Falasɗinu ya ambato wasu ganau suna cewa Yahudawan sun shiga Masallacin ne ta ƙofar Al-Mugharbah da ke yammacinsa.

Yahudawan, waɗanda suka samu kariya daga wurin dakarun Isra'ila, sun riƙa yin abubuwan da za su tunzura mutanen da ke cikin masallacin yayin da suka gudanar da ibadun Talmud.

Ganau sun ce an ƙara tsaro a Tsohon Birnin Ƙudus da hanyoyin zuwa masallacin.

0336 GMT —Isra'ila ta yi luguden wuta a Gaza a yayin da Kwamitin Tsaro na MDD ya gudanar da taro

Isra'ila ta kai sabbin hare-hare a yankin Rafah da ke kudancin Gaza bayan Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya gudanar da taro kan wani hari da ta kai a sansanin 'yan gudun hijira wanda ya jawo mata Allah wadarai daga faɗin duniya.

Masu aiko da rahotanni na kamfanin dillancin labarai na AFP a Rafah sun ruwaito cewa Isra'ila ta kai sabbin hare-hare da sanyin safiyar Laraba, awanni kaɗana bayan ganau da kuma wata majiyar tsaro ta Falasɗinu sun ce tankokin yaƙin Isra'ila sun shiga cikin tsakiyar birnin.

"Yanzu haka mutane suna cikin gidajensu ba su fita ba saboda jirage marasa matuƙa na Isra'ila suna harbe duk wanda ya fito waje," a cewar wani mazaunn yankin mai suna Abdel Khatib.

Shugaban Amurka Joe Biden ya gargaɗi Isra'ila kan ƙaddamar da manyan hare-hare a Rafah, sai dai gwamnatinsa ta dage cewa har yanzu Isra'ila ba ta wuce gona da iri ba.

Gaza

2300 GMT — Algeria za ta gabatar wa Kwamitin Tsaro na MDD ƙudirin kira a tsagaita wuta a Gaza

Ƙasar Aljeriya ta yaɗa wani ƙuduri a Majalisar Dinkin Duniya da ke neman a tsayar da yaƙin da ake yi a Gaza nan-take da kuma umarnin Isra’ila ta tsayar da kutsen sojoji a kudancin birnin Rafah ba tare da jinkiri ba.

Ƙudirin wanda kamfanin dillacin labarai na AP ya samu ya kuma buƙaci duka ɓangarorin da ke yaƙin su mutunta tsagaita wutar. Ya kuma yi kira da a sako gaba ɗaya mutanen da aka yi garkuwa da su lokacin da Hamas ta kai hari sansanin sojan Isra'ila da kuma matsugunan Yahudawa a kudancin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

Haka kuma ƙudirin ya nemi a yi aiki da ƙudurce-ƙudurce na baya da suka yi kira a buɗe duka iyakokin yankin da kuma barin kayan agaji su isa ga mutane miliyan 2.4 da suke tsananin buƙatar abinci da sauran agaji.

Matakin da ake shirin gabatarwa ya ce "mummunan yanayin da ake ciki a Gaza yana barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin da kuma duniya baki ɗaya."

Ƙudirin ya ce "Lallai Isra'ila ta dakatar da harin da sojojinta ke kaiwa da ma duk wani mataki a Rafah."

Ya kuma yi Allah-wadai da "kisan kan mai-uwa-da-wabi da fararen-hula ciki har da mata da yara da wuraren amfanin fararen hula" ya kuma jaddada cewa majalisar ta nemi duka ɓangarorin su yi aiki da dokokin duniya da suka buƙaci kare fararen-hula.

Amurka tana kare ƙawarta Isra'ila a lokuta da dama, sannan ta hau kujerar na-ƙi a ƙudurori da dama da ke neman a tsagaita wuta a Gaza.

RAFAH, GAZA - 28 ga MAYU: Wani Bafalasɗine yana jimamin mutuwa kuma yana kuka kusa da gawawwakin waɗanda Isra'ila ta kashe a ranar 28 ga watan Mayu, 2024 a yammacin Rafah a Gaza. / Hoto: AA

2100 GMT — Mexico na neman a saka ta a ƙarar da Afirka ta kai Isra'ila kan kisan kiyashi a Gaza

A hukumance, ƙasar Mexico ta buƙaci ta shiga cikin ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar da Isra'ila a gaban Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta Duniya (ICJ) inda take zarginta da aikata laifukan kisan ƙare-dangi a Gaza.

"Mexico ta yi aiki da Sashe na 63 na Kotun, inda ta gabatar da 'Buƙatar Yin Hukunci' kan Isra'ila game da aikata laifukan kisan kiyashi a Gaza bisa ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar," a cewar wata sanarwa da Kotun ICJ ta fitar.

Sashe na 63 ya bai wa kowace ƙasa da ta amince da shi ta shiga ƙarar kamar yadda Mexico ta yi.

A jawabin Mexico, ta ce "kisan kiyashin" da Isra'ila take yi ya haɗa da kisan ɗimbin mutane da lalata al'adunsu da kawar da su daga doron ƙasa.

TRT World