Dakarun sojin Isra’ila sun sake rusa wani kauyen Falasdinawa na Larabawa Makiyaya da ke kudancin yankin Negev a Yammacin Kogin Jordan.
A ranar Litinin ne sojojin Isra’ila suka dira a kauyen tare da rusa shi a karo na 216, kamar yadda Aziz al Touri, wani mamba na Kwamitin Kare kauyen al Araqib ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Turkiyya, Anadolu.
Al Touri ya jaddada cewa mazaunan kauyen sun dauki aniyar sake gina gidajensu nasu, kamar yadda suke yi a duk lokacin da dakarun sojin Isra’ila suka lalata musu shi.
Gidajen da ke Al Araqib, wanda wasu iyalai 22 na Falasdinawa ke zaune a ciki, an gina su ne da katako da roba da kuma langa-langa.
A shekarar 2010 ne aka fara rusa kauyen. Hukumomin Isra’ila sun yi ikirarin cewa yankin da kauyen yake ya fada karkashin ikon kasarsu ne.
Mazauna kauyen Al Araqib Larabawa ne 'yan asalin Isra’ila da aka raba su da muhallansu tun a shekarar 1951, a lokacin da kasar Isra’ila da ke fadada ta yi ikirarin cewa yankinta ne.
A wani rahotonta na baya-bayan nan, Zochrot, wata kungiya mai zaman kanta a Tel Aviv ta ce al Araqib shi ne na farko da aka gina tun zamanin Daular Usmaniyya, kuma mazauna wajen ne suka sayi filayen garin.
Hukumomin Isra’ila sun bukaci kwace iko da filayen tare da korar mazauna wajen, inda gomman kauyuka da al’ummomin Larabawa Makiyaya ke fuskantar barazana a yankin Negev, kamar yadda kungiyar Zochrot ta ce.