Wani harin makamin roka na Rasha ya faɗa kan wani shagon shan shayi a wani ƙauye inda fararen hula 51 suka mutu, a ɗaya daga cikin hare-hare mafiya muni da suna faru a ƙasar cikin tsawon watannin da aka shafe ana yaƙi, kamar yadda Shugaba Volodymyr Zelenskyy da wasu manyan jami'ai suka faɗa a birnin Kiev.
Harin ya faru ne a lokacin da Zelenskyy ke halartar wani taro na kusan shugabannin ƙasashen Turai 50 a Sifaniya, inda aka tattauna batun yadda Ukraine za ta samu ƙarin goyon baya daga wajen ƙawayenta.
Ya yi Allah wadai da harin wanda aka kai ƙauyen Hroz a matsayin "wata ƙazamar aika-aika da Rasha ta yi" kuma "wani aiki na ta'addanci."
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa Andrii Yermak da gwamnan Kharkiv, Oleh Syniehubov sun ce wani yaro ɗan shekara shida na daga cikin waɗanda suka mutu a harin, inda suka ƙara da cewa an ji wa wasu mutum bakwai ɗin rauni.
Ƙauyen Hroza, wanda ke da yawan al'umma kusan 500 kafin yaƙin, yana can ne a yankin Kharkiv da ke arewa maso gabashin ƙasar.
Kusan mutum 60 ne a cikin kantin shan shayin suke addu'o'i bayan kammala wata jana'iza, a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na ƙasar, Ihor Klymenko, wanda ya faɗi adadin waɗanda suka mutun.