A wata sanarwa, mai magana da yawun kungiyar Falasdinawa ta Islamic Jihad, Tariq Silmi, ya ce, “Rundunoninmu a shirye suke su yi amfani da kowace irin hanya wajen mai da martani kan zaluncin gungun ‘yan mamaya."/ Hoto: Reuters / Hoto: AFP

Isra’ila ta kashe akalla mutane 12 a hare-hare ta sama da ta kai Zirin Gaza, inda sojin kasar suka ce manufarsu ita ce far ma mambobin kungiyar Falasdinawa ta Islamic Jihad.

Jami’in Falasdinu ya ce a ranar Talata, mambobi uku na kungiyar, da kuma akalla farar hula tara, wadanda suka hada da yara hudu sun rasa rayukansu.

Ma’aikatar Lafiya ta Falastinu ta ce akwai mata da yara cikin wadanda suka rasu. Amma ba ta bayar da karin bayani kan wadanda abin ya rutsa da su ba. Sama da mutane 20 ne suka samu raunuka.

Rundunar soji ta Isra’ila ta ce ta kai hari ne kan gidajen manyan kwamandojin kungiyar ta Islamic Jihad.

A wata sanarwa, kungiyar al Quds Brigades, wanda reshe ne na kungiyar fafutuka ta Palestinian movement, ta ce matan kwamandojin da ‘ya’yansu suna cikin wadanda aka kashe a hare-haren.

Ganau sun ce makamai sun sauka kan rufin gidan da ke Gaza, da kuma wani gida a kudancin birnin Rafah.

Sojojin Isra’ila sun ce harin ta sama, wanda aka yi wa lakabi da “Operation Shield and Arrow," manufarsa shi ne kan Khalil Bahtini, kwamandan kungiyar ta Islamic Jihad a arewacin Gaza; da Tareq Izzeldeen, mai aiki tsakanin mambobin kungiyar bangaren Gaza da Gabar Yamma, da kuma Jihad Ghannam, sakataren majalisar kungiyar ta Islamic Jihad.

Sanarwar ta kara da cewa kwamandojin uku su ne ke da alhakin harin roka da aka harba wa Isra’ila a baya-bayan nan.

Kakakin sojin Isra’ila, Richard Hecht ya fada wa ‘yan jarida cewa rundunar sojin ta "cimma abin da take son cimmawa" a harin cikin cikin daren, wanda ya ce ya kunshi jiragen sama 40.

An jiyo karar fashewar makamai daga harin saman, wanda ya fara bayan karfe 11 na dare a agogon yankin, har tsawon awa biyu, a cewar rahoton dan jaridar AFP.

Dangin wani shugaban kungiyar Islamic Jihad, Khalil Bahtini, suna jimami kusa da gawarsa, a mutuwaren asibitin Al Shifa a Birnin Gaza bayan harin isra’ila ya kashe shi a gidansa. / Hoto: AFP

An takaita zirga-zirga

Harin saman na sojin Isra’ila ya zo ne bayan ta-da-kayar-baya tsakanin Isra’ila da Falastinawa a yankin Gaza da ke cikin kangin kasar Isra’ila, wanda kungiyar Hamas ke mulka.

Isra’ila da mayakan Gaza sun yi musayar wuta, bayan mutuwar Khader Adnan a gidan yarin Isra’ila, wanda ya yi yajin cin abinci na kwana 87 bayan Isra’ila ta kama shi bisa zargin alaka da kungiyar ta Islamic Jihad.

Kasa da mako daya da ya wuce, kungiyar ta Islamic Jihad ta sanar da tsagaita wuta a yankin Gaza, wanda aka cimma da taimakon kasar Masar da Majalisar Dinkin Duniya, da kasar Qatar, bayan faruwar sabon rikici a yankin.

Ranar Talata, kungiyar ta Falastinu, ta ce Isra’ila ta “bijire wa duka yunkurin masu shiga tsakani”. Don haka kungiyar ta sha alwashi “daukar fansar shugabanninta” da aka kashe a hare-haren.

A wata sanarwa kuma, shugaban Hamas, Ismail Haniyeh ya ce, "kashe shugabannin a wannan hari na cin amana,ba zai kawo tsaro ga ‘yan mamaya ba, sai dai ma ya zuzuta wutar masu yakar zaluncin Isra’ila".

Kakakin kungiyar ta Hamas, Hazem Qassem, ya yi gargadin cewa Isra’ila ce ke da alhakin “duka wani abin da wannan hari zai haifar".

Yayin da suke tsoron hare-hare daga Gaza sakamakon harinsu, sojin Isra’ila sun fitar da sanarwar da ke ba da shawara ga mazauna wuraren da ke nisan kilomita 40 daga Gaza, su zamo kusa da famakar harin bam da aka ayyana.

Kasar Isra’ila da mayakan Gaza sun sha gwabza yaki tun lokacin da kungiyar Hamas ta karbi iko da yankin na Gaza a shekarar 2007.

A rikicin kwanaki uku a watan Augustan bara, an samu rasuwar mutane 49 a bangaren Falastinawa, amma Isra’ila ba ta rasa ko mutum daya ba.

Zuwa yanzu, harin ranar Talata ya sanya adadin Falastinawan da sojoji da ‘yan sandan Isra’ila suka kashe, ya kai mutum 120 a iya wannan shekara kawai.

A dai wannan lokacin, ‘yan Isra’ila 19 aka kashe, a kirgen AFP wanda ya duba majiyoyin hukuma daga bangarorin biyu.

Isra’ila ta ce farmakin soji a Gabar Yamma da kogin Jordan da suka mamaye, yana da manufar dakile hanyoyin ayyukan kungiyoyin tirjiya, da hana faruwar hare-harensu a gaba.

Falastinawan kuwa suna kallo hare-haren a matsayin dabarun cigaba da mamayar da kasar Isra’ila ke yi tsawon shekaru 56. Danniyar haramtacciya ce kuma suna neman ceto yankunan da aka mamaye ne don kafa kasar falastinawa mai ‘yanci a nan gaba.

TRT World