Masana kimiyya ba su fara fargaba ba a yanzu, amma suna saka ido sosai kan lamarin. / Hoto: AFP

Wata gagarumar fashewa a sararin subahana, za ta samar da wani tururi da ya fi na fashewar bam din Hiroshima sau ɗaruruwa. Wani haske mai tsanani kamar na rana zai samu. Da jijjiga mai ƙarfi da za ta iya rusa duk wani abu a kan hanyarta.

Abin zai yi kamar ana zancen tashin duniya, amma ana maganar wani dutsen da ke shawagi a sararin samaniya ne da aka gano kwanan nan, wanda girmansa ya kai filin ƙwallo da a yanzu ake hasashen akwai yiwuwar kashi 1 cikin 100 cewa zai iya cin karo da duniyarmu ta Earth nan da shekara takwas.

Akwai yiwuwar tasirin irin wannan lamari na iya lalata illahirin birni, ya danganta da wajen da dutsen ya faɗa.

Masana kimiyya ba su fara fargaba ba a yanzu, amma suna saka ido sosai kan lamarin.

Babban masanin kimiyya na ƙungiyar The Planetary Society, Bruce Betts ya ce "A wannan gaɓar, batu ne na mayar da hankali, da tattaro duk wasu abubuwa da ake buƙata wajen sanya ido kan lamarin."

Abin da ba a faye ganowa ba

Hukumar da ke sa ido kan sararin samaniya ta Chile El Sauce Observatory ce ta fara gano dutsen, wanda aka saka masa suna 2024 YR4 a ranar 27 ga watan Disamban 2024. Yanayin haskensa ne ya sa 'yan sama jannati suka yi ƙiyasin cewa faɗinsa ya kai daga tsakanin kamu 130 zuwa 300, wato mita 40 zuwa 90.

Zuwa jajiberin sabuwar shekara ne bayaninsa ya isa kan teburin Kelly Fast, wata jami'ar tsaro ta hukumar sararin samaniyar Amurka, NASA, a matsayin wani abin damuwa.

"Abubuwan da aka gano, sai kuma su sake ɓacewa. Amma shi wannan akwai alamar ba zai ɓace ba," ta faɗa.

Bayanin barazanar da ke tattare da lamarin na ta ƙaruwa, kuma a ranar 29 ga watan Janairu, Ƙungiyar Ƙasa da Ƙasa da ke Gargaɗi kan Duwatsun da ke Shawagi a Sararin Samaniya (IAWN), ta fitar da wata sanarwa.

Sabbin lissafe-lissafen da cibiyar bincike ta NASA Jet Propulsion Laboratory sun nuna cewa akwai yiwuwar kashi 1.6 cikin 100 na dutsen astiriyod din zai faɗa duniyar Earth ranar 22 ga watan Disamban 2032.

Sanarwar IAWN ta bayyana cewa idan har dutsen ya faɗo, akwai yiwuwar zai iya faɗawa a ɗaya daga cikin waɗannan wuraren, gabashin Tekun Fasifik, kudanci da arewacin Amurka, Tekun Atalantika, Afirka, Tekun Arebiya da kuma Kudancin Asiya.

2024 YR4 ya shafe shekara huɗu yana zagaye a tsakanin duniyoyin Unguwarmu ta Rana, Solar System, kafin daga bisani ya wuce ta gaban Mars da Jupiter.

A yanzu, yana yin nesa da Earth - ba zai sake matsowa kusa da ita ba sai nan da shekarar 2028.

"Abin shi ne ba wai lallai sai ya ci karo da Earth ba, wataƙila ma nan da watanni ko shekaru kaɗan masu zuwa yiwuwar hakan ta kau gaba ɗaya," in ji Betts.

Wani abu irin haka ya faru a 2004 ya faru da Apophis, wani dutsen astiriyod da a baya aka yi hasashen akwai yiwuwa ta kashi 2.7 cikin 100 ya faɗo cikin duniyar Earth a 2009. Daga baya wasu bayanan suka kore yiwuwar hakan.

Yiwuwar yin ɓarna

Rabon da a samu wani lamari da dutsen astiriyod ya yi ɓarna ya faru ne shekara miliyan 66 da suka wuce, a lokacin da wani astiriyod mai faɗin mil shida ya jawo wani hunturu a duniya, tare da kawar da halittun kakannin ƙadangaru da ake kira dinosaurs da kuma kashi 75 na dukkan halittu.

Sai dai shi ma dutsen astiriyod na 2024 YR4 an saka shi a cikin rukunin "city killer", wato wanda ka iya rusa birni.

Betts ya ce "Idan ka sanya shi a saman birnin London ko New York, to zai rusa kafatanin birnin da ma kewayensu."

Amma misalin da zai fi yin daidai na kurkusa shi ne wanda ya faru a shekarar 1908 da ake kira Tunguska Event, lokacin da wani astiriyod mai girman mita 30 zuwa 50 ya fashe a samaniyar Siberia, abin da ya jawo kawar da bishiya miliyan 80 a fadin kilomita 2,000.

Tamkar wancan lamarin, ana sa ran dutsen 2024 YR4 zai fashe a sararin samaniya, maimakon faɗowa ƙasa har ya haƙa rami.

"Za mu iya lissafin zafin tururin da zai samar... ta hanyar amfani da gudunsa," in ji Andrew Rivkin, wani ɗan sama jannati a cibiyar bincike ta Johns Hopkins Applied Physics Laboratory.

An ƙiyasta cewa, idan har dutsen astiriyod na 2024 YR4 ya fashe, to zai samar da zafi da turirin kusan megaton takwas ko ma fiye da sau 500 na abin da bam din Hiroshima ya samar.

Idan kuma ya fashe a sararin samaniyar teku, to tasirin ba zai zama mai tayar da hankali ba, sai dai idan ya faru a gabar teku ne daidai inda zai iya jawo tsunami.

Za mu iya dakatar da shi

Labari mai dadi da ƙwararru suka jaddada shi ne cewa muna da isasshen lokacin shiryawa.

Rivkin ya jagoranci binciken shirin NASA na 2022 DART, wanda ya yi nasarar kawar da wani astiriyod daga kan hanyarsa ta hanyar amfani da jirgin sama jannati - wata dabara da ake kira da "kinetic impactor."

Shi wannan astiriyod din ba ya yi wa duniyar Earth wata barazana, abin da ya sa ya dace da a yi gwajin a kansa ke nan.

"Ban ga dalilin da zai sa ba za a bi irin wannan dabara a kan wannan ba," ya ce. Babbar tambayar ita ce ko manyan ƙasashe za su iya zuba kuɗaɗe a cikin wannan shiri idan har suka tabbatar yankinsu ba ya fuskantar barazana."

Amma akwai wasu tarin dabarun da za a iya gwadawa.

Amma idan duka ba su yi aiki ba, to gargadi na dogon zango shi ne ya kasance hukumomi za su iya kwashe abubuwa masu muhimmanci daga yankin da ake hasashen zai faɗa.

Fast ya ce "kar wanda ya ji tsoron wannan lamari. Za mu iya gano wadannan abubuwa, mu yi hasashe kuma mu iya shiryawa.

TRT World