A ranar Laraba Falasɗinawa suke gudanar da tarukan tunawa da cika shekaru 76 da korar su ta ƙarfi da aka yi daga yankin da ya zama Isra'ila a yanzu, lamarin da ya zama gwagwarmayar ƙasa a gare su.
Amma a hanyoyi da dama, wancan rikici da ya afku ya dusashe idan aka kwatanta da bala'in da suka tsinci kansu a ciki a yau.
Falasɗinawa na kiran wannan lamari da "Nakba" kalmar da a harshen Larabci ke nufin "Bala'i".
Kimanin Falasɗinawa 700,000 - mafi yawan su ba su taɓa shaida yaƙi ba - sun gudu ko an kore su daga gidajensu kafin da lokacin fafata yaƙin Larabawa da Isra'ilawa a 1948, wanda a bayansa ne aka kafa ƙasar isra'ila.
Bayan yaƙin, Isra'ila ta hana su komawa gidajensu.
Maimakon haka, sai suka zama 'yan gudun hijira na din-din-din da a yanzu kusan miliyan 6 ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira a Lebanon da Syriya da Jordan da Gaɓar Yammacin Kogin Jodan da Isra'ila ta mamaye.
A yanzu a Gaza, 'yan gudun hijira da zuriyarsu ne kaso uku cikin huɗu na jama'ar da ke zaune a yankin.
Ƙin amincewar da Isra'ila ta yi na abin da Falasɗinawa suka kira haƙƙinsu ne babban dalilin rikicin, kuma shi ne abin da aka fi tattaunawa don samar da zaman lafiya, amma aka gaza cim ma matsaya shekaru 15 da suka wuce.
A yanzu Falasɗinawa na tsoron maimaituwar wannan bala'i ko ma wanda ya fi shi muni.
A yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare, Falasɗinawa na hawa ababen hawa, motoci ko jakai ko tafiya a kasa, inda suke barin matsugunansu a Gaza.
Hotuna daga wurare da dama da ake kwashe jama'a tawaga-tawaga a tsawon watanni bakwai da aka shafe ana gwabza yaƙi, na zama iri ɗaya da baƙaƙen hotunan da aka ɗauka a 1948.
Mustafa al Gazzar mai shekara 81 a yanzu, yana iya tuna tafiyar wata guda da iyalansa suka yi daga ƙauyensu wanda a yanzu ya zama tsakiyar isra'ila a kudancin garin Rafah, a lokacin yana dan shekara 5. A wasu wuraren ana kai musu harin bam ta sama, a wasu wuraren suna shige wa ƙarƙashin ramukan da aka haka a ƙarƙashin bishiyu don kwanciya.
Al Gazzar da a yanzu ya tsufa, an tilasta masa sake yin hijira a ƙarshen makon da ya gabata, a wannan lokacin tanti ya koma da zama a Muwasi, wani waje da ke gaɓar teku da kusan Falasɗinawa 450,000 ke rayuwa cikin mummunan yanayi.
Ya ce halin da suke ciki ya fi na 1948 muni, a lokacin da Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya Mai Kula da Falasɗinawa na iya kawo musu abinci da kayan amfanin na yau da kullum.
"Fatana a 1948 shi ne na dawo ƙauyenmu, amma a yau fatana shi ne na kuɓuta da rayuwata," in ji shi. "Ina rayuwa a cikin wannan fargaba," ya faɗa yana zubar da hawaye. "Ba zan iya samo komai ga yarana da jikokina ba."
Mummunan yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza ya yi ajalin sama da Falasɗinawa 35,000, kamar yadda jami'an lafiya na yankin suka bayyana, wanda shi ne kisa mafi yawa da aka yi a tarihin rikicin.
Yaƙin Isra'ila a Gaza na baya-bayan nan ya tursasa wa Falasdinawa miliyan 1.7 - kusan kashi uku cikin huɗu na jama'ar yankin - barin gidajensu, sau da yawa a lokuta daban-daban. Wannan ya zama fiye da ninkin waɗanda suka gudu a lokacin Nakba a 1948.
Ƙasashen duniya na adawa da korar dubban ɗaruruwan Falasɗinawa daga matsugunansu a Gaza - tunanin da masu tsatssauran ra'ayi a Isra'ila ke yi wa kallon "Gudun hijirar ganin dama".
A Gaza, Isra'ila ta ƙaddamar da hari mafi muni da kashe mutane a baya-bayan nan, a wasu lokutan suna jefa bam mai nauyin kilogram 900 a kan yankunan da ke da jama'a da yawa.
An mayar da dukkan yankin zuwa wajen ɓaraguzan gine-gine da rusassun hanyoyi, da yawansu na ɗauke da bama-baman da ba su fashe ba.
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa an yi ɓarnar da ta kai ta dala biliyan 18.5 a Gaza, wanda ya kai yawan ma'aunin tattalin arzikin wato GDP da yankin Falasɗinawa ya samu a shekarar 2022.
Wannan lissafi na watan Janairu ne, a farkon fara kai hare-haren Isra'ila a Khan Younus, kafin ta koma kai wa Rafah.
Yara Asi, mataimakin Farfesa Bafalasɗine a Jami'ar Central Florida da ya yi bincike kan illar da aka yi wa fararen-hula a yakin, ya ce "Yana da wahala sosai" a iya hakaito irin ƙoƙarin da ƙasashen duniya za su yi don sake gina Gaza.
Tun kafin yakin ma, Falasɗinawa da yawa sun yi magana kan Nakba da ake ci gaba da gani, wadda a cikinta Isra'ila ta tursasa musu barin Gaza daYammacin Gaɓar Kogin Jordan da Gabashin Kudus, yankunan da ta mamaye a lokacin yaƙin 1967 da Falasɗinawa suka nemi kafa ƙasarsu a nan gaba.
Tun kafin yaƙin ma sun dinga ɗaukar matakan nuna wariya irin su nuna gidajen da za a rushe da sake gina unguwannin, abinda ake wa kallon irin matakan gwamnatin nuna wariyar launin fata.
Asi da wasu na tsoron wata sabuwar Nakba na afkuwa, amma ita wannan a hankali ake yin ta.
Asi ya ce "Ba za a kira wannan raba mutane da matsugunansu ta karfi da yaji ba a wasu al'amuran. Za a kira hakan gudun hijira, za a kira hakan wani abu daban."
"Amma asali dai, mutane ne da ke son zama, waɗanda suka yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun zauna ɗin tsawon shekaru a yanayin da ba zai yiwu ba, a ƙarshe sun kai ga matakin da rayuwa ba za ta yiwu a cikin sa ba."