Wakilan al’ummar Musulmai da aka gayyata zuwa Fadar White House sun tattauna batutuwa da dama da suka hada da yadda ake nuna "zalunci da rashin bin ka'idar tsarin mulki" kan Musulman Amurka da kuma yadda ake danganta su da masu son tashe-tashen hankula da nuna musu wariya.
A ranar Talata ne manyan jami'ai gwamnatin Biden suka shirya wani taro, wanda ya gudana kwana guda bayan da shugaban kasar Joe Biden ya yi taron bikin karamar sallah ta Eid al-Fitr tare da shugabannin addinin Musulunci.
Wakilan al'ummar Musulman Amurka da suka halarci taron sun hada da Imam Mohamed Magid, daraktan Kungiyar Hadin kai na American-Islamic CAIR-NJ da daraktan sashen kula da harkokin gwamnatin Amurka da addinin Musulunci Robert McCaw da kuma shugaban gidauniyar 'yan Shi'a Rahat Husain.
A yayin taron, "shugabannin Musulmai sun bayyana kalubalen da al'ummominsu ke fuskanta tare da bayar da shawarwarin tunkarar matsalar tsangwama da duk wani nau'in kiyayya da nuna kyama," a cewar Fadar White House.
"Jami'an gwamnatin Biden da Harris sun mika godiyar su ga mahalarta taron bisa jagorancin da suka yi tare da jaddada kudirin shugaban kasar na dakile duk wani nau’in nuna kyamar Musulunci," in ji sanarwar.
A zaman taron, Robert McCaw ya bukaci jami'an gwamnatin Biden da su janye " rashin adalci da bin ka'idar doka, da a asirce ta sanya mutum miliyan 1.5 akasari Musulmai, a jerin mutanen da gwamnati ke bincike a kansu ba tare da sanarwa ko bin ka'ida ba."
Matakin da Hukumar Tsaro ta Sirri ta Amurka ta dauka na haramta wa Magajin Garin New Jersey, Musulmin da ya fi dadewa kan mukamin halartar bikin Sallah na Fadar White House "shi ne misali na baya-bayan nan kan yadda masu sa ido ke cutar da mutanen da ba su ji ba su gani ba," in ji wakilan CAIR.
"Barka da zuwa gida"
Fadar White House ta ce zaman na daga cikin wani bangare na kokarin da shugaban kasar ke yi a kwamitinsa da ke yaki da nuna wariya da kyamar addinin Musulunci da kuma duk wasu nau'ukan nuna son kai da tsangwama a cikin Amurka.
Yayin da ya karbi bakuncin liyafar bikin sallah a ranar Litinin, Biden ya gaisa da wadanda suka halarci taron, yana mai cewa, "Barkanku da zuwa gida."
Fadar White House "tana sane da irin wakilci da gudunmowar da al’ummar Musulmai suka bayar ga al'ummarmu a matsayin malamai da injiniyoyi da likitoci da lauyoyi da 'yan kasuwa har ma da mata da maza 'yan majalisa" in ji Biden.
Ya kara da cewa "Musulmai sun nuna jarumtaka sosai a cikin rundunonin sojin Amurka da sauran hukumomin tsaro."
Liyafar bikin sallar da Biden ya jagoranta ya fuskanci mummunar suka ta kafafen yada labarai bayan da Hukumar Tsaro ta Sirri ta hana Magajin Garin Musulmi, Mohamed Khairullah halartar taron.
Daga baya ya fitar da wata sanarwa yana mai cewa lamarin "ya matukar nuna kyamar Musulunci daga wasu hukumomin tarayya kasar."