Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da takwaransa na ƙasar Iraƙi Abdul Latif Rashid da firaiministan ƙasar Mohammed Shia al Sudani yayin wata ziyarar aiki da ya kai birnin Bagadaza.
A yayin da shugaban Turkiyya ya isa Bagadaza ranar Litinin domin tattaunawa kan batutuwa daban-daban, ɓangarorin biyu sun ƙulla yarjejeniya da za ta amfane su.
Da yake bayyana yarjejeniyar a matsayin wani "muhimmin ci gaba", shugaban Turkiyya ya shaida wa taron manema labarai na haɗin-gwiwa da Firaiministan Iraƙi Mohammed Shia al Sudani cewa: "Na yi amannar cewa ziyarar da na kawo da kuma yarjeniyoyin da muka ƙulla yanzu za su kasance wata sabuwar turba ta kyautata dangantaka tsakanin Turkiyya da Iraƙi".
Firaiministan Iraƙi Al Sudani ya sanar cewa Turkiyya da Iraƙi sun ƙulla yarjeniyoyi 24.
A gaban shugaban Turkiyya da Firaiministan Iraƙi, wakilan ƙasashen biyu sun ƙulla yarjeniyoyi na haɗin-kai tsakanin Iraƙi, Turkiyya, Qatar, da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).
“Babu bambanci tsakanin tsaron Iraƙi da na Turkiyya”
Erdogan ya ƙara da cewa haɗa-gwiwa kan sha'anin tsaro da yaƙi da ta'addanci yana ɗaya daga cikin manyan batutuwan da suka tattauna a ziyarar da ya kai Iraƙi.
Ya ce Turkiyya ta yi maraba da matakin da Iraƙi ta ɗauka na ayyana ƙungiyar ta'addanci ta PKK a matsayin wadda aka haramta a ƙasar.
Shugaban Turkiyya ya jaddada kira ga dukkan ɓangarori su guji yin duk wani abu da zai ƙara dagula halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya.
Firaiministan Iraƙi Al Sudani ya ce ya amince da shugaban Turkiyya a game da kyautata dangantakar tsaro tsakanin maƙwabtan biyu.
“Babu bambanci tsakanin tsaron Iraƙi da na Turkiyya,” in ji shi a taron manema labarai a suka gudanar da Bagadaza.
Firaiministan Iraƙi ya jaddada cewa ƙasarsa ba za ta bari wata ƙungiyar ta'addanci ta yi amfani da ƙasar wajen kai hari kan makwabtanta ba, inda yake magana a kan ƙungiyar ƴan ta'adda ta PKK.
Tattaunawa kan yaƙin Gaza da batutuwan da suka shafi yankin da ma ƙasashen duniya
A ganawar da ya yi da Abdul Latif Rashid tun da farko ranar Litinin, shugaban Turkiyya da takwaransa sun tattauna kan yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza da batutuwan da suka shafi yankinsu da na ƙasashen duniya, da kuma yaƙi da ta'addanci.
Erdogan ya bayyana cewa Turkiyya tana fatan Iraƙi ta kawar da ƴan ƙungiyar ta'adda ta PKK sannan ya jaddada buƙatar ganin ƙasar ta kawar da duk wani nau'i na ta'addanci.
Kazalika ya bijiro da muhimmancin dawo da dangantaka tsakanin Bagadaza da Gwamnatin Yanki ta Ƙurdawa a Iraƙi da tabbatar da ganin Turkawa sun samu matsayin da ya dace domin wanzar da zaman lafiya a ƙasar.
Haɗin-kai don goyon bayan Gaza
Haka kuma shugaban Turkiyya ya bayyana yunƙurin da ake yi na kawo ƙarshen zaluncin da Isra'ila take yi a Gaza da jaddada muhimmancin haɗin-kan ƙasashen Musulmai wajen tabbatar da hakan.
Erdogan ya kai ziyarar ce tare da rakiyar Ministan Harkokin Wajen ƙasar Hakan Fidan, da Ministan Harkokin Cikin Gida Ali Yerlikaya, da Ministan Tsaro Yasar Guler, da Daraktan Sadarwa Fahrettin Altun, da babban mai ba shi shawara Akif Cagatay Kilic da sauran manyan mutane.
Wannan ne karon farko da Shugaba Erdogan ya kai ziyara Iraƙi cikin shekaru 12.