An sha samun bore da Allah-wadai kan rikicin na Isra'ila a Gabashin Birnin Kudus/ Hoto AA

Dakarun Isra’ila sun kai hari Masallacin Kudus, na uku mafi tsarki a duniya, da ke Gabashin birnin na Kudus.

Sun yi amfani da bama-bamai da gurneti sannan suka rika lakada wa Falasdinawa masallata duka lamarin da ya kai ga jikkatar da dama daga cikinsu, a cewar ganau da kuma kungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent.

Wani bidiyo da aka dauka daga cikin masallacin wanda ya karade soshiyal midiya ya nuna mata da kananan yara suna ta ihu suna neman taimako, yayin da dakarun na Isra’ila suke kai musu harin.

Wannan hari ya sanya fargabar yiwuwar sake barkewar rikici tsakanin bangarorin biyu.

Palestinian Red Crescent ta ce ta aika da tawagar likitoci domin duba lafiyar mutanen da suka jikkata.

"Ina zaune a kan kujera ina karatun Alkur’ani lokacin da lamarin ya faru," in ji wata tsohuwa a hirarta da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Wata tsohuwa da aka jikkata ta ce tana tsaka da karatun Alkur'ani aka kai harin/AA

Tsohuwar ta fashe da kuka yayin da take kokarin bayyana halin kaduwar da suka shiga.

Masu sallar sun rika rera taken kyamar Isra’ila yayin da dakarun kasar suke tilasta musu fita daga masallacin.

Kazalika sojojin Isra’ila sun lalata tagogin masallacin daga bangaren yamma, a cewar ganau.

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Isra’ila ta fitar ta ce ta kama Musulmai da ke yin itikafi a masallacin.

Kamfanin dillancin labaran Falasdinu ya ce dakarun Isra’ila sun jikkata Musulmai da dama wadanda suka kwashe dare suna yin ibada a masallacin na Kudus.

TRT World