Sojojin Isra'ila sun saka shinge na karfe domin hana Kiristoci wucewa

Dakarun Isra'ila sun kai hari kan Kiristoci da suka je coci domin halartar bikin "Holy Fire" a Gabashin Birnin Kudus ranar Asabar.

Kiristocin mabiya darikar Orthodox, ciki har da fada-fada na coci, sun yi tattaki zuwa cocin Apocalypse inda ake rera wakoki da yin kalamai na addini domin gudanar da al'ada ta "wuta mai tsarki ".

Sun rika kallon yadda Larabawa mabiya darikar Orthodox ke tafiya cikin shauki suna kida kan titin tsohon Birnin inda suke gasar daukar hotuna da wayoyinsu.

A lokacin da suka isa cocin Apocalypse, Kiristocin sun yi ta jiran "wuta mai tsarki", daya bayan daya kowa ya rika kunna kyandir yayin da aka kada karaurawa a coci.

Wasu daga cikin Kiristoci wadanda suka so zuwa bikin, wanda aka gudanar saboda ana zaton a ranar ce "aka gicceye Yesu ya mutu sannan aka tashe shi, " kamar yadda koyarwar addinin Kirista ta nuna.

'Yan sandan Isra'ila sun toshe hanyar da ke zuwa cocin da ke tsohon Birnin Kudus kuma ba su bar Falasdinawa da Kiristoci wadanda ba 'yan kasa ba su wuce.

Sojojin Isra'ila sun sanya shinge na karfe domin hana Kiristoci wucewa, ciki har da mata dattawa da dama.

Kadan daga cikin malaman coci da Kiristoci mabiya Orthodox aka bari suka shiga cocin.

Kamar yadda hotunan da Anadolu ta samu suka nuna, wasu Kiristoci, ciki har da mata, na amfani da karfi wurin halarta bikin, inda dakarun Isra'ila suka far wa wasu daga cikinsu.

An bayyana cewa har da wani Malamin Kirista cikin mutanen da sojojin Isra'ila suka yi wa duka har wani ya suma.

Sai dai wata sanarwa da 'yan sandan Isra'ila suka fitar, ta ce akwai dubban mutane da suka je tsohon birnin, kuma "yan sanda na iya kokarinsu domin samar da tsaro ga wadanda suka halarci taron."

Sanarwar ba ta bayyana ko 'yan sanda sun ci zarafin Kiristoci ba wadanda suka je yin addu'oi.

TRT Afrika da abokan hulda