Tamkar dai kakannin kakanninta da suka gabata, ƴar sama jannatin Daular Larabawa Nora AlMatrooshi ta shafe tsawon lokaci a rayuwarta tana sha'awar duk abin da ya shafi kallon taurari, da kuma mafarkin zuwa Duniyar Wata.
A wannan makon, ta zama mace Balarabiya ta farko da ta kammala makarantar hororwa ta Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, ta kuma shirya tsaf don ketawa cikin Sararin Subhana.
AlMatrooshi mai shekara 30, takan tuna wani darasi da aka koya mata a makarantar firamare a kan sararin samaniya, inda malamarta ta kwatanta musu yadda ake zuwa Duniyar Wata, ta hanyar tsara kayan ƴan sama jannati da jirgin sama jannati da kuma tanti.
AlMatrooshi ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa "Da muka fita daga cikin tantin sai muka ga ta kashe wutar ajinmu. Ta lulluɓe komai na wajen da mayafi launin toka, sai ta ce mana ai a kan Duniyar Wata muke."
"Wannan ranar ta tsuma ni kuma ta maƙale a cikin raina. Nakan tuna abin d ana raya a raina, 'Wannan abu da ƙayatarwa yake. Ina so na yi hakan a gaske, ina so na je Duniyar Wata a zahiri.' To daga nan ne komai ya fara," ta ba da labari, a yayin da take sanye da tufafin da ƴan sama jannati kan saka masu launin shuɗi da rubutun sunanta da tutar ƙasarta ta UAE a jiki.
AlMatrooshi, wadda injiniya ce wacce ta samu horo ta kuma yi aiki a masana'antar man fetur, na ɗaya daga cikin ƴan sama jannati biyu da Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta UAE, [UAESA] ta zaɓa a shekarar 2021 don shiga cikin wani shiri da za a yi musu a NASA ta Amurka.
A yanzu bayan da ta shafe shekara biyu tana aiki tuƙuru — ciki har da koyon yadda ake tafiya a sararin samaniya — AlMatrooshi da abokin aikinta da shi ma ɗan ƙasarsu ne Mohammad AlMulla, da wasu sauran mutum 10 a ajin nasu na samun horo, sun zama cikakkun ƴan sama jannati.
Tawagar mai suna "The Flies," a yanzu sun cancanci yin bulaguron NASA zuwa Tashar Ƙasa da Ƙasa ta Sararin Samaniya [ISS], da tafiyar shirin Artemis zuwa Wata, kuma idan abubuwa sun yi daidai yadda ake sa rai to har Duniyar Mars za su je.
A farkon shekarar nan, hukumar UAESA ta sanar da shirye-shiryenta na gina wani ƙyaure na musamman mai iya hana iska shiga cikin jirgin sama jannati, da zai iya zagaya Wata.
"Ina so na ga ɗan'adam ya je inda bai taɓa zuwa ba. Ina so ɗan'adam ya koma Duniyar Wata, kuma ina so ɗan'adam ya je gaba da Wata," in ji AlMatrooshi.
Duk da cewa AlMatrooshi ce ta farko da ta kammala makarantar horo ta NASA, akwai sauran mata Larabawa da suka taka rawa a ayyukan da suka shafi binciken sararin samaniya, ciki har da ƴar Saudiyya Rayyanah Barnawi, wacce ta je tahsar ISS bara, da kuma ƴar Misira da Labanon Injiniya Sara Sabry, wacce tana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi balaguron samaniya na shirin Blue Origin a 2022.
Saka hijabi a balaguron samaniya
AlMatrooshi, wadda ke sanya hijabi saboda kasancewar ta Musulma, ta yi bayani kan yadda NASA ta samar da dabarun da za su ba ta damar rufe kanta bayan ta saka tufafin da hukumar ta yarda a saka da kuma hular kwano, waɗanda ake kira da Extravehicular Mobility Unit, ko EMU.
"Da zarar ka saka tufafin EMU, to za ka sanya hular sadarwa mai bututun magana da abin sauraro, waɗanda za su rufe ma gashi," ta ce.
Ƙalubalen ya fara ne a lokacin da AlMatrooshi ta cire hijabinta da ta saba sakawa kafin ta ɗora hular sadarwan.
Baya ga haka kuma, akwai abubuwan da ke ƙara sa abin ya yi tsananin, saboda ba a iya amfani da komai idan aka saka tufafin EMU sai abin da ya dangance su.
"Daga baya dai injiniyoyin da ke samar da kayan sun ɗinka mini wani hijabi, da zan iya sakawa bayan na sanya tufafin, sannan sai na ɗora hular sadarwar ta yadda gashina zai rufu. Don haka na ji daɗi sosai na kuma gode kan wannan abin da suka yi mini," a cewar AlMatrooshi.
A yanzu da ta samu tufafinta tsaf a kammale, AlMatrooshi za ta shirya wa tafiya zuwa sararin samaniya da sauran abokan aikinta ƴan sama jannati.
Ƙarnin ci gaban kimiyya na Malaman Musulunci
NASA ta shirya ganin ɗan'adam ya sake sauka a Duniyar Wata a shekarar 2026 a shirinta na Artemis 3.
"A gaskiya zama ɗan sama jannati na da wahala sosai, ko a wane addini kake bi ko yankin da ka fito," ta shaida wa AFP.
"Ba na jin idan kasancewar mutum Musulmi zai ƙara sa abin ya yi tsauri. Amma kasancewa ta Musulma ya sa na tuna irin gudunmawar da kakannin kakannina suka bayar, daga cikin manyan Malaman Musulunci kuma masana kimiyya waɗanda suka wanzu ɗaruruwan shekaru da suka wuce da suka nazarci taurari."
"Zama ta ƴar sama jannati kamar ɗorawa ne a kan abin da suka fara dubban shekaru da suka wuce," in ji AlMatrooshi.
Malaman Musulunci sun samu ci gaban kimiyya tun yankin Turai ba su san komai ba, kuma ilimin taurari na daga cikin waɗanda Malaman Musulunaci suka fi mayar da hankali a kan a wancan lokacin.
Musulmai masana ilimin tarurari sun samar da tsantsar ilimin da ya shafi sararin samaniya daga tsakanin ƙarni na 8 zuwa na 15.
Al-Farghani da Jafar Ibn Muhammad Abu Mashar al-Balkhi da Al-Battani da Ḥasan Ibn al-Haytham [wanda shi ne farkon wanda ya fayyace yadda mutane ke fahimtar haske] na daga cikin fitattun malaman falaƙi da masana kimiyya na wancan lokacin.