Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Mohamed bin Zayed sun tattauna kan yadda wadannan yarjeniyoyi za su samar da karin damarmaki a tsakaninsu / Hoto: AA

Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun sanya hannu kan yarjejeniyoyin kasuwanci 13 da suka kai na $50.7 billion, a cewar Ma'aikatar Sadarwa ta Turkiyya.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, ma'aikatar ta ce dukkan bangarorin biyu sun amince su kafa Majalisar Koli ta Musamman, wadda shugaban Turkiyya da takawaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa za su jagoranta.

Dangantakar Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa ta kai babban mataki na hadin gwiwa sakamakon wannan yarjejeniya, in ji sanarwar.

"Kazalika bangarorin biyu sun amince su fadada dangantakarsu a fannin makamashi, sufuri, ababen more rayuwa, kasuwanci ta intanet, harkokin kudi, lafiya, abinci, yawon bude ido, harkokin gidaje, harkokin gine-gine, tsaro, da kirkirarriyar basira wati artificial intelligence har ma da inganta fasaha," a cewar sanarwar.

Ta kara da cewa: "Yarjejeniyar da aka kulla a wadannan bangarori ta kai ta $50.7 bn jimilla."

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce kasarsa za ta tabbatar cewa dangantakarsu da Hadaddiyar Daular Larabawa ta yaukaka a matakin na kololuwa.

Ya yi jawabin ne a yayin da ya gana da shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan a fadarsa ta Al Watan da ke Abu Dhabi.

Da yake bayyana gamsuwarsa a game da dangantakar diflomasiyya da suka kulla shekara 50 da suka gabata, Erdogan ya ce Turkiyya na fatan kyautata alaka da Hadaddiyar Daular Larabawa a fannin zuba jari, tsaro, makamashi mara gurbata muhalli da sufuri.

“Yarjeniyoyin hadin gwiwar da muka sanya wa hannu za su ba mu damar kyautata dangantakarmu zuwa mataki na musamman,” in ji Erdogan, inda ya kara da cewa: “Za mu hada taro kan Ciniki da Zuba Jari bayan damuna a Istanbul domin gabatar da wannan yarjejeniya ga 'yan kasuwarmu.”

TRT World