Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu a Gaza ta yi gargadi kan durkushewar harkokin lafiya a fadin Zirin Gaza sakamakon rashin isassun gadajen kwantar da marasa lafiyar da hare-haren Isra’ila suka jikkata, a asibitoci.
A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ce “babu gadajen kwanciya a asibitoci. Mutanen da suka ji raunuka da sauran marasa lafiya duk a kasa suke kwance a yayin da Isra’ila ke zafafa kai hare-haren rashin tausayi.”
Ta ce ci gaba da yanke lantarki da ruwa da man fetur da Isra’ila ke yi yana saka rayukan marasa lafiya cikin “matukar hatsari kuma hakan zai jawo mummunan bala’i na lafiya da muhalli.
“Za mu dora alhakin dukkan asarar rayuka da ta marasa lafiya a kan mamayar Isra’ila, saboda yadda hakan ke yin tasiri a lalata tsarin lafiya da raunana shi,” sanarwar ta kara da cewa.
Ma’aikatar ta kuma yi gargadin cewa yin shirun da ake yi zai iya rusa halin tsarin lafiya da ake ciki a Gaza, “kuma dole ne a dauki wani mataki ba tare da bata lokaci ba na tabbatar da shigar da kayayyakin asibiti.”
Sanarwar hukumomin lafiyar ta Gaza na zuwa ne a yayin da Isra’ila ke tsaka da ci gaba da kai hare-hare Gazan, lamarin da ya yi sanadin sanya dubban mutane a cikin bukatar kula da lafiyarsu da gaggawa.
Ba za mu kula da majinyatan Falasdinu ba - Isra'ila
Ministan Lafiya na Isra'ila Arbel a cikin wasikar da ya aike wa Firaminista Benjamin Netanyahu a ranar Laraba, ya sanar da cewa ya ba da umarnin a dakatar da kula da ƴan ƙungiyar Hamas da suka ji rauni a asibitocin gwamnati, kamar yadda Anadolu ya rawaito jaridar Yedioth Aharonoth ta kasar tana cewa.
A cikin wasiƙar tasa, Arbel ya ce, "Tsarin kiwon lafiyar zai mayar da hankali ne kawai a kan sojojin Isra'ila a wannan lokaci mai wahala da kuma shiryawa abin da zai zo nan gaba," inda ya ƙara da cewa ba zai taɓa bari a duba ƴan ƙungiyar Hamas da suka jikkata ba a asibitocin gwamnati.
Yi wa Gaza ƙawanya
A ranar Litinin ne Ministan Tsaro na Isra’ila Yoav Gallant, ya bayar da umarnin “yi wa Gaza ƙawanya baki daya” a lokacin da ake tafka fada tsakanin kasarsa da kungiyar Falasdinawa ta Hamas.
Hamas ta ƙaddamar da wasu hare-hare da ta kira Operation Al-Aqsa Flood, a ranar Asabar, inda ta dinga harba makaman rokoki zuwa Isra’ila ta ƙasa da ta sama da ta ruwa.
Ta ce ta kai harin ban mamakin ne a matsayin martani kan dirar mikiyar da ake yi wa Masallacin Kudus a Gabashin Birnin Kudus ɗin, da kuma yadda ake samun ƙaruwar kai wa Falasdinawa hare-hare a yankin.
Ita kuma rundunar sojin Isra’ila ta ƙaddamar da wasu hare-haren na Operation Swords of Iron a kan Hamas a matsayin martani.