Baya ga mutuwar mutane 62 a bana a yankunan da ke fama da rikici a duniya, an kuma jikkata wasu ma'aikatan jinkai 84 tare da yin garkuwa da 34 a cewar wasu bayanai./ Hoto: SafeguardingHC

An kashe ma'aikatan bayar da agaji akall 62 a bana a fadin duniya, a cewar wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya (MDD).

Rahoton na zuwa ne a daidai lokaci da Majalisar ke shirye-shiryen cika shekaru 20 bayan mummunan hari da aka kai hedikwatarta da ke birnin Bagadaza na kasar Iraki.

MDD ta ware 19 ga watan Agustan kowace shekara a matsayin ranar jinkai ta duniya, yayin da take tunawa da harin kunar bakin waken da ya yi sanadin mutuwar mutum 22, ciki har da na Sergio Vieira de Mello, wanda shi ne babban kwamishinan kare hakkin bil adama na Majalisar kuma shugaban tawagar MDD na kasar.

Baya ga mutuwar mutane 62 a wannan shekara a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula a duniya, an kuma jikkata wasu ma'aikatan agaji 84 tare da yin garkuwa da 34, a cewar kididdigar Cibiyar Samar da Bayanan Tsaron ma’aikatan jinkai, wanda kamfanin ba da shawarwari na Humanitarian Outcomes ya tattaro.

Kazalika, adadin ma’aikatan da suka mutu baki daya a shekarar 2022 ya kai mutum 116.

A tsawon shekaru, Sudan ta Kudu ta kasance wuri mafi hatsari ga ma'aikatan agaji a duniya. Ya zuwa ranar 10 ga watan Agusta, an kai hare-hare sau 40 kan ma'aikatan jinkai a kasar, inda aka yi asarar rayukan mutum 22, a cewar ofishin kula da ayyukan jinkai na MDD.

Kasar da ke biye mata ita ce Sudan, inda aka kai hare-hare sau 17 kan ma'aikatan bayar da agaji, sannan mutane 19 ne suka mutu a bana.

Ba a taba samun adadi mai yawan wannan ba tun bayan rikicin Darfur daga shekarar 2006 zuwa 2009.

Sauran kasashen da ma'aikatan jinkai suka mutu sun hada da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Mali da Somaliya da Ukraine da kuma Yemen.

"Hatsarin da muke fuskanta ya wuce tunanin dan Adam," a cewar wani rahoton hadin gwiwa da wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suka hada da Doctors of the World da Action Against Hunger da Handicap International tare da taimakon kungiyar Tarayyar Turai.

Tashe-tashen hankula sun mamaye ayyukan ma'aikatan jinkai na cikin gida

A kowace shekara, sama da kashi 90 cikin 100 na mutanen da ke mutuwa a hare-haren da ake kai wa na cikin gida ma’aikatan jinkai ne, a cewar kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa.

A bana, ranar jinkai ta duniya ke cika shekaru 20 da kai harin bam a Bagadaza a Otal din Canal, wajen da ya kasance hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya a babban birnin kasar Iraki.

An kai harin ne a shekara ta 2003 a cikin yanayin tashin hankalin mamayar da Amurka ta jagoranta wajen hambarar da Saddam Hussein.

"Ranar Jinkai ta Duniya da harin bam da aka kai Otal din Canal a ko da yaushe za su kasance wasu yanayi na jimami a gare ni da sauran mutane da dama," a cewar shugaban agaji na Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths.

"Rashin hukunci kan wadannan laifuka tabo ne ga gare mu baki daya."

Yayin da tashe-tashen hankula ke dada karuwa a duniya, Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana kokarin taimaka wa kusan mutane miliyan 250 da ke zaune a yankunan da ke fama da rikici. Yanayin ya ninka na shekarar 2003 sau 10.

TRT World