An tilasta wa Apple fara amfani da cazar da ke iya daukar mafi yawan wayoyi ne da aka fitar a shekarar 2012. Hoto: Reuters

Kamfanin Apple ya fitar da sabuwar wayar iPhone ranar Talata kamar yadda ya saba baje-kolinta a karshen bazarar kowace shekara, inda yake yunkurin ganin ya bai wa mutane dalilin sayen wayar mai dauke da sabbin fasahohi.

Baje-kolin na zuwa ne a lokacin da kamfanin Apple ya yi fama da faduwa a cinikinsa na bara cikin kowane wata uku har sau uku a jere, saboda ba a samu cinikin sayar da wayoyin iPhone sosai ba.

Apple ya kaddamar da iPhone 15, 15 Plus, 15 Pro da 15 Pro Max. Farashin iPhone 15 ya fara ne daga $799, yayin da 15 Plus za ta kai $899. iPhone 15 na da inci 6.1, ita kuwa 15 Plus tana da inci 6.7.

Masu sharhi na ganin sabuwar iPhone 15 din ta yi ne tsada sosai ne saboda sabbin abubuwan da ta zo da su a jikinta.

Cikin abubuwan da aka inganta a jikin wayar a bana har da karfin kyamararta ta daukar hoto inda za ta fi ta kowacce da aka taba yi a baya.

Daya daga cikin manyan sauyin da kamfanin Apple ya sanar game da sabuwar wayar shi ne sabon salon caza ta.

Kamfanin ya samar da tsarin yadda za a iya amfani da cazar USB-C da aka fi amfani da ita a yawancin wayoyi, har ma da komfutocin Mac da iPad.

An tilasta wa Apple fara amfani da cazar da ke iya daukar mafi yawan wayoyi ne da aka fitar a shekarar 2012, don amfani da ita a jikin iPhone 15 saboda wata doka da kasashen Turai suka sanya da za ta fara amfani a shekarar 2024.

Kasuwa ta yi kasa

Kamar dai yadda aka saba gani a tattare da kamfani Apple da sauran kamfanonin wayoyin komai da ruwanka, ba a saka ran cewa sabon samfurin iPhone din zai kawo wani gagarumin sauyi ba a fannin fasaha.

Sauye-sauyen da za a gani a jikin wayar iPhone 15 ba za su wuce abubuwan da za su kara farashinta a kan na baya ba, da suka hada da inganta kyamararta da batiri da kuma manhajar chip da ke makale a wayar.

Sannan akwai yiwuwar sauya fasalin wayar ta yadda allon wayar zai kasance da tsari mai kyau, wanda kamfanin Apple ya kira da “Dynamic Island” ta wajen da sakonnin manhajoji suke bayyana - wani tsari da aka samar a wayoyin da ya kera bara na Pro da Pro Max.

Idan dai har jita-jitar da ake yi ta tabbata gaskiya, to kyamarar hoton iPhone 15 Pro da Pro Max za su kasance masu daukar hoto ne rangadadau ko da daga nesa sosai aka dauke shi.

Karfin kyamarar hoton zai iya daukar hoto ta hanyar janyo shi sau 6, amma duk da haka ba zai kai na wayar Samsung Galaxy S22 Ultra da ke iya janyo hoton har sau 10 ba, amma zai dara na iPhone 14 Pro da Pro Max sau uku.

Inganta kyamarar da aka yi na daga cikin dalilan da suka sa kamfanin Apple ya kara farashin wayoyin Pro da Pro Max.

A yanzu dai za a zuba ido a ga yawan mutanen da za su yi kokarin sayen sabon samfurin ganin yadda ake fama da matsalolin tattalin arziki a sassa daban-daban na duniya sakamakon tasirin da annobar korona ta jawo da yake addabar mutane har yanzu.

TRT World