Ɗan takarar shugaban Amurka a jam'iyyar Republican Donald Trump ya gabatar da kansa a matsayin mai fafutukar kare 'yan kirifto sannan ya caccaki jam'iyyar Democratic game da yunƙurinta na yin garambawul a wannan harka.
Ya bayyana haka ne a wurin neman tallafin kuɗin yaƙin neman zaɓe a birnin San Francisco, kamar yadda majiyoyi uku da suka halarci taron suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
"Ya ce zai zama shugaban ƙasa na 'yan kirifto," in ji Trevor Traina, wani shugaban kamfanin fasaha da ke San Francisco kuma tsohon jakadan gwamnatin Trump a Austria, a hirarsa da Reuters ranar Juma'a.
Masu hada-hada da kuɗin kirifto na ci gaba da ƙoƙarin jan hankalin 'yan siyasar Amurka a yayin da hukumomi suka matsa wajen sanya ido a wannan harka, musamman bayan wasu manyan kamfanonin kirifto sun yi faɗuwar-guzuma a 2022 lamarin da ya haddasa gagarumar asara ga waɗanda suka zuba jari a harkar tare da bankaɗo almundahanar da ke cikinta.
Donald Trump ya ce kuɗin kirifto yana da muhimmanci sannan ya jaddada goyon bayansa ga masu mu'amala da shi, a cewar wata 'yar kwamitin mata na Jam'iyyar Republican Harmeet Dhillon.
Dhillon ta ce Trump, wanda zai fafata da Shugaba Joe Biden na jam'iyyar Democratic a zaɓen ranar 5 ga watan Nuwamba, bai yi bayani dalla-dalla kan manufarsa game da kuɗin kirifto ba.
Trump ya samu tallafin $12m domin gudanar da yaƙin neman zaɓe a taron da kamfanonin fasaha na David Sacks and Chamath Palihapitiya suka gudanar.
Manyan shugabannin kamfanonin kirifto irinsu Coinbase, da masu zuba jari a kirifto da suka haɗa da Tyler da Cameron Winklevoss na cikin waɗanda suka halarci taron, a cewar Dhillon.
Shugaba Biden ya sha alwashin haɗa gwiwa da majalisun dokokin Amurka don samar da doka mai ƙarfi da za ta sanya ido kan hakar kirifto a ƙasar.