A ranar 29 ga watan Oktoba ne Turkiyya ta yi bikin cika shekara 100 da zamowar ƙasar Jamhuriya, wanda Mustafa Kemal Ataturk, mutumin da ya mayar da kasar tafarkin zamani, ya ayyana ta a matsayin jamhuriya.
An yi bukukuwa a faɗin biranen da ke Turkiyya, inda mutane suke dinga baje-kolin abubuwan ci gaban fasaha da tsaro ta hanyar yin fareti daban-daban.
A cikin shekara 100 na nasarorin da Turkiyya ta samu, an samu ci gaba a kimiyya da fasaha da haɗin kai da kyawawan abubuwan da suka faru a baya da kuma wanda za a iya yi a nan gaba.
SOLOTURK, wata tawagar Rundunar Sojin Sama ta Turkiyya ta yi wani faretin shawagi da jiragen yaƙi ta saman ginin Anitkabir, wani gidan adana kayan tarihi na abubuwan da suka shafi wanda ya samar da Jamhuriyar Turkiyya Mustafa Kemal Ataturk, a yayin bukuwan yin bikin cikar Turkiyya shekara 100 da zama Jamhuriya.
Sannan katafaren jirgin ruwan yaƙi na Turkiyya mai suna TCG Anadolu ma ya yi nasa shawagin a cikin Mashigar Ruwa ta Istanbul duk a cikin bikin murnar cikar Turkiyya da zama jamhuriya.
Wasu jiragen ruwa na yaƙin 100 ne suka yi wannan shawagi tare da katafaren jirgin na TCG Anadolu.
Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kalli yadda katafaren jirgin ruwan yaki na TCG Anadolu na Turkiyya yake tafiya a cikin Mishigin Tekun Istanbul tare da saurana jiragen ruwan 100 duk don bikin cikar Turkiyya shekara 100 da zama jamhuriya.
Faretin da jiragen ruwa na yaƙi 100 suka yi a cikin mashigin Ruwan Istanbul ya kuma haɗa da shawagin jiragen sama da helikwaftoci. Sannan tawagar SOLOTURK ma ta yi nata faretin ta sama.
Baya ga tawagar SOLOTURK da na jiragen ruwa na yaƙi, akwai wasu jiragen saman na taurarin Turkiyya da su ma suka yi faretin.
Shi ma kamfanin TOGG, wanda shi ya fara ƙera motoci masu aiki da lantarki, ya zuba motocin nasa sun yi fareti inda suka bi ta saman Gadar Yavuz Sultan Selim a Istanbul a jere reras, duk a cikin bikin cikar Turkiyya shekara 100 da zama jamhuriya.
A can cibiyar Sojin Sama ta Sivrihisar da ke Eskisehir, kuwa, dumbin mutane ne su 100 suka jeru reras riƙe da tutocin Turkiyya inda suka yi ƙawanya da ya nuna alamar rubuta 100.