Manufofin kudi na Turkiyya za su janyo zuwan karin masu zuba jari daga kasashen waje a 2024, in ji Daraktan JP Morgan Stefan Weiler, yayin wata tattaunawa da Reuters.
Bayan gagarumar nasarar zabe a watan Mayu, manufofin kudi na Shugaba Recep Tayyip Erdogan sun fara janyo hankalin masu zuba jari na kasashen waje.
"Daga bangarenmu, muna kallon Turkiyya a matsayin wadda za ta samu babban labari a shekara mai zuwa," in ji Weiller, Shugaban Sashen JP Morgan da ke kula da Basussuka ga Kasashen Tsakiya da Gabashin Turai da Gabas ta Tsakiya da Afirka (CEEMEA) yayin tattaunawa da Reuters.
Babban Bankin Turkiyya karkashin Hafize Gaye da aka naɗa ta a watan Yuni, ya fara tsawaita kudin ruwa nan da nan.
Kudin ruwa da kafin zabe yake a kaso 8.5, a yanzu ya kai kashi 40.
'Haihuwar da mai ido'
A 2024, gwamnati ana sa ran bayar da lamunin kasa da kasa na dala biliyan 10, wanda zai kai adadin na wanna shekarar. Weiler ya ce yana dakacin ganin karbar bashi sosai daga kamfanoni da bankuna.
"Matukar kasuwanni na cikin yanayi mai kyau a duniya, to Turkiyya ta saurari shekarar kwararowar masu zuba jari daga waje," in ji Weiler.
Ya kara da cewa "Tuni aka fara samun zuwan masu zuba jari, hakan na nufin an samu haihuwar ɗa mai ido a Turkiyya."
Yayin da yake batu kan zaben ranar 31 ga Maris, ya ce "Ina jin kananan zabuka da za a gudanar a nan gaba a Turkiyya za su kara karfafa gwiwar zuwa Turkiyya don zuba jari,"
Haka kuma, JP Morgan na sa ran za a samu habaka a fannin bayar da bashin tsabar kudade a duniya a shekara mai zuwa. Kuma adadin da za a samu zai i kowanne a tarihi, amma za a samu raguwar hakan daga China.
Sabuwar shekarar ha'anin kudi a Turkiyya
Bayan nada Mehmet Simsek a matsayin Ministan Baitulmali da Kudi, an samu sabbin muhimman bayanai a fagen sha'anin tattalin arziki a Turkiyya.
Simsek ya nuna muhimmancin gaskiya, daidaito da hasashe a matsayin manyan jogogin manufofin tattalin arzikin Turkiyya.
Tun zabukan watan Mayu, an dauki kwararan matakan gyara don karfafa yaki da hauhawar farashi da babban bankin ke yi, tare da ganin hakan ya samu wajen zama a manufofin gwamnati.
Simsek ya bayyana saukar da farashi da tsari a sha'anin kudi da gyare-gyare a matsayin manyan ginshikan habaka tattalin arzikin Turkiyya a matsakaicin zango na tsakanin 2004-2026.